Yan Bindiga Sun Kashe Alhaji Muhammad Kudu, Sadukin Masarautar Lafiagi
- Yan bindiga sun halaka Alhaji Muhammad Kudu, Sadukin Masarautar Lafiagi a Jihar Kwara
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe basaraken ne a hanyar Lapai da Lambata a Jihar Niger
- Gwamnan Jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya yi tir da kisan basaraken ya kuma zaburar da hukumomin tsaro su kawo karshen maharan
Jihar Kwara - Wasu yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun kashe Saduki na Masarautar Lafiagi, Alh Muhammed Kudu, Leadership ta rahoto.
Lafiagi ne hedkwatar karamar hukumar Edu a Jihar Kwara.
Rahotanni, a cewar Intelregion sun bayyana cewa an kashe Kudu ne a harin bindiga tsakanin tsohuwar Lapai da Lambata a Jihar Niger.
Gwamnan Jihar Kwara ya yi ta'aziyya
A sakon ta'aziyyarsa, gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana mutuwar babban ma'aikacin FIRS din a matsayin abin bakin ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi tir da kisar gillar da aka yi wa Kudu da kakkausan murya a cikin sakon da babban sakataren watsa labaransa, Tafiya Ajakaye ya fitar.
"Ina mika sakon ta'aziyya ga mutanen masarautar Lafiagi, Mai Martaba Sakin Lafiagi, Alhaji Mohammed Kudu Kasu, da iyalan Sadukin Lafiagi mai rasuwa bisa wannan abin bakin cikin.
"Abin bakin cikin ya yi yawa. Muna sake kira ga hukumomin tsaro cewa kada su sassauta wurin kawar da yan ta'addan da ke asarar rayuka da kowane dalili," gwamnan ya ce cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin.
"Muna addu'ar Allah ya bawa iyalansa hakurin jure rashinsa a yanzu da gaba. Muna addu'ar Allah ya kawo mana zaman lafiya da tsaro," gwamnan ya ce.
Yan Bindiga Sun Sace Sarki A Najeriya Bayan Sun Harbi Direbansa
A wani rahoton, yan bindiga sun sace mutane hudu ciki har da basarake na Iku Quaters, Oniku na IKu, a Ikare Akoko ta Jihar Ondo, Cif Mukaila Bello, Leadership ta rahoto.
Tare da basaraken, an cewar wata majiya, an kuma sace Mr Adeniran Adeyemo, Mr Bashiru Adekile da Cif Gbafinro.
Channels TV ta rahoto cewa an sace su ne daren ranar Alhamis a Ago Panu na Owo-Ikare Road, a hanyarsu ta zuwa Akure daga Ikare.
Asali: Legit.ng