Tsohon Shugaban Ƙasa, Yakubu Gawon, Ya Rasa Babbar Yayarsa A 90

Tsohon Shugaban Ƙasa, Yakubu Gawon, Ya Rasa Babbar Yayarsa A 90

  • Babbar yaya ga tsohon shugaban ƙasa a lokacin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon watau Maryamu Lami, ta rasu
  • Marigayayya maryamu ta rasu ne a wani Asibitin Jos, babban birnin jihar Filato tana da shekara 90 a duniya ranar 3 ga watan Agusta
  • Kafin rasuwarta, Maryamu Lami ta kasance matar kwamishinan yan sanda, Mr S.K. Dimka, ta bar ƴaƴa uku da jikoki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jos - Tsohon shugaban ƙasa lokacin mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya yi rashin babbar yayarsa mai suna, Maryamu Lami Ɗinka.

Marigayya Maryamu, wacce ta kasance yar uwa ɗaya tilo da ta rage wa Janar Gawon a raye, ta mutu ne ranar uku ga watan Agusta a wani Asibitin Jos, babban birnin jihar Filato.

Yar uwar tsohon shugaban ƙasan ta rasu ne bayan fama da rashin lafiya na tsawon mako shida, babbar ɗiyar mamaciyar, Elizabeth Rimdans, ta tabbatar da mutuwar ga Daily Trust ranar Asabar a Jos.

Kara karanta wannan

Hotuna: Ɗan Sanata Ahmad Sani Yarima ya angwace da budurwarsa ƴar ƙasar Somalia a London

Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gawon.
Tsohon Shugaban Ƙasa, Yakubu Gawon, Ya Rasa Babbar Yayarsa A 90 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Elizabeth Rimdans, ta bayyana cewa maharfiyar ta ta rasu ta bar ƴaƴa uƙu, jikoki da dama da ƴaƴak jikoki da yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika Misis Elizabeth ta ayyana mutuwar mahaifiyar su da wani babban rashi ga baki ɗaya iyalan gidan su.

Ta ƙara da bayanin cewa:

"Ba bu abin da zai maye gurbin raashin mahaifiyar mu, zamu cigsba da rayuwa ne muna tuna ta a kowane lokaci. Ta kasance mai kirki wacce a ko yaushe take son haɗa kan mutane.

Kafin rasuwarta, marigayya Maryamu ta kasance matar aure ga tsohon kwamishinan yan sanda, Mr S.K. Dimka, kuma mamba da shugaban wasu ƙungiyoyi da dama.

Daga cikin irin waɗan nan ƙungiyoyi akwai Red Cross, ƙungiyar matasan matan kiristoci da ƙungiyar Littafin Kirista Bibul ta Najeriya da sauran su.

A wani labarin na daban kuma An fallasa wani shirin Gwamna Wike, da yuwuwar zai yaƙi Atiku ya koma bayan wannan Ɗan Takarar a 2023

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: A Karon Farko, Gwamna Wike da Atiku Abubakar Sun Sa Labule A Gidan Wani Tsohon Minista

Yayin da ake ganin jam'iyyar PDP ta fara shawo kan rikicinta ganin Wike da Atiku sun zauna, wata majiya ta ce akwai matsala har yanzu.

Wani jagora a PDP ya ce gwamna Wike ka iya komawa yana yaƙar Atiku kuma ba zai sauya sheƙa daga jam'iyya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel