2023: Da Yuwuwar Gwamna Wike Ba Zai Goyi Bayan Zaɓen Atiku Ba, Majiya

2023: Da Yuwuwar Gwamna Wike Ba Zai Goyi Bayan Zaɓen Atiku Ba, Majiya

  • Yayin da ake ganin jam'iyyar PDP ta fara shawo kan rikicinta ganin Wike da Atiku sun zauna, wata majiya ta ce akwai matsala har yanzu
  • Wani jagora a PDP ya ce gwamna Wike ka iya komawa yana yaƙar Atiku kuma ba zai sauya sheƙa daga jam'iyya ba
  • A karon farko bayan saɓanin da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani da abokin takara, an ga Wike da Atiku sun gana

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - A karon farko tun bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa da zaɓen abokin takara wanda ya haddasa rikici a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike sun gana jiya Alhamis a Abuja.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin PDP da Wike sun gana ne da nufin lalubo hanyar ɗinke ɓarakar da ke tsakanin su.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
2023: Da Yuwuwar Gwamna Wike Ba Zai Goyi Bayan Zaɓen Atiku Ba, Majiya Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Sai dai ganawar jiga-jigan biyu ba wani abun a zo a gani bace, wani shugaban PDP ya ce da yuwuwar Wike ba zai mara wa Atiku baya ba matuƙar ba'a shawo kan matsalolin yadda ya dace ba.

Wata majiya da jaridar ta samu, ta bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Wike ba zai fice daga PDP ba amma zai iya zama mai tarwatsa wa. Nan ba da jimawa ba, mutanen da Atiku ya watsar a wajen zaɓen tawagar yaƙin neman zaɓe ko wani abu, su ne Wike zai jawo a jiki su yaƙi ɗan takaran."
"Zai zama ɗan hamayya a cikin jam'iyyar hamayya, yana goyon bayan takarar Peter Obi a sirrin ce, zai yi makamancin abin da Rauf Aregbesola ya yi wa PDP a jihar Osun."
"Duk da Aregbesola bai sauya sheƙa ba, amma ya umarci masoyansa su koma bayan Ademola Adeleke. Da yuwuwar Wike zai yi makamancin haka yayin yaƙin neman zaɓe."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: A Karon Farko, Gwamna Wike da Atiku Abubakar Sun Sa Labule A Gidan Wani Tsohon Minista

Atiku da Wike sun san muhimmancin 2023

Sai dai wani babban jigon PDP ya bayyana cewa:

"Atiku da Wike sun san Abinda ke a hannu, sun san cewa zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a mutu ko ai rai ne a wurin PDP kuma akwai buƙatar su sasanta kan su domin mu tunkari zaɓen a dunƙule."

A wani labarin kuma Ɗan Majalisar Tarayya na zango biyu da wasu Jiga-Jigan PDP Sun Koma LP

Tsohon ɗan majalisar dokokin tarayya, Chief Linus Okorie, da wasu jigogi a jam'iyyar hamayya PDP sun koma LP a Ebonyi.

Daga cikin masu sauya sheƙan har da wani ɗan takara da ya nemi tikitin gwamna karkashin PDP da kuma tsohon kwamishina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel