Ta’aziyya: Abin da Khalifa Muhammadu Sanusi II ya fada game da rashin Alhaji Bashir Tofa

Ta’aziyya: Abin da Khalifa Muhammadu Sanusi II ya fada game da rashin Alhaji Bashir Tofa

  • Mai martaba Muhammadu Sanusi ya yi wa jama’ar Kano da Arewa ta’aziyyar rashin Bashir Othman Tofa
  • Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II yace mutuwar Dattijon rashi ne ga Najeriya gaba daya
  • A sakon ta’aziyyar da ya aiko, tsohon Sarkin ya bayyana yadda Alhaji Tofa ya kaunaci zuri’ar Khalifa Sanusi I

Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da Kwankwaso Tuwita, ya wallafa bidiyon ta’aziyyar da Muhammadu Sanusi II ya yi na rashin Bashir Othman Tofa.

A shafinsa na Twitter a ranar Talata, wannan Bawan Allah ya daura ta’aziyyar da tsohon Sarkin Kano ya yi wa al’umma a kan wannan babban rashi da aka yi.

Bayan salati ga Annabi Muhammad (SAW), Muhammadu Sanusi II ya yi ta ambatar ‘InnalilLahi wa inna ilaihi raji’un’ domin jimamin rashin Alhaji Bashir Tofa.

Kara karanta wannan

Yadda Marigayi Tofa ya jajirce domin hana a tsige Sanusi da kafa sababbin masarautu a Kano

Mai martaba Sanusi II yace shi karon kan shi ya yi rashin babban masoyi wanda shi da mahaifinsa suka kaunace shi da mahaifinsa da kakansa, Sanusi I.

Jawabin Sanusi II a bidiyo

“Ina yi mana gaba daya ta’aziyyar rashin Alhaji Bashir Othman Tofa, wannan rashi ne ga kasarmu baki daya.”
“Rashi ne ga Kano wanda ta rasa shugaba, jagora wanda zai tsaya a kan martabarta, mutuncinta da kare martabar al’ummarta da dukiyarta.”
Khalifa Muhammadu Sanusi
Tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II Hoto: BBCNewsHausa
Asali: Facebook

“Ni kai na wannan rashi ne gare ni babba na masoyi wanda da shi da mahaifinsa, suka nuna kauna da soyayya da Sarki Khalifa (Muhammadu Sanusi) da Ciroma da Daniya da zuri’armu baki daya.”
“Wannan rashi da jimami dukan a mu. Mu na rokon Allah (SWT) ya gafarta masa. Allah ya sa ayyukansa na alheri su bi shi, Allah ya yafe masa kura-kurensa."

Kara karanta wannan

‘Diyar tsohon Sarki Sanusi ta taya iyayenta murnar cika shekara 30 da aure da tsofaffin hotuna

- Muhammadu Sanusi II

A wannan bidiyo, an ji Sanusi II ya ba iyalin Marigayin hakuri, tare da kira ga mutane su cigaba da yi masa addu’ar gamawa da Duniya lafiya.

A karshe Muhammadu Sanusi II ya yi addu’a Allah ya jikan mu idan lokacin mutuwarmu ya zo.

Abin da mutane ke fada a Twitter

Ameen ya Allah. Allah ya taimaki Sarki.

- Mahmoud Abbas Sanusi

Khalifanmu, Sarkinmu, Shugabanmu

- Najeeb Wali

Tabbas Khalifa ya yi rashin masoyi, Allah ya jikan Dattijo, Alh. Bashir Othman Tofa.

- M. Gote

Tofa ya kwanta dama

A ranar 3 ga watan Junairu, 2022, aka samu labarin rasuwar dattijon Arewa, Bashir Othman Tofa wanda ya cika a gidansa a ranar Lahadin da ta gabata.

Mun kawo maku takaitaccen tarihin Alhaji Bashir Tofa wanda kowa yake yabo bayan rasuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel