Biyan Kudin Fansa ya Jawo aka Lakadawa Fasinjojin Jirgin Kaduna-Abuja Mugun Duka

Biyan Kudin Fansa ya Jawo aka Lakadawa Fasinjojin Jirgin Kaduna-Abuja Mugun Duka

  • Bidiyon da aka fitar da ya nuna ana lakadawa fasinjojin Abuja-Kaduna duka, ya girgiza mutane
  • Rahoto ya nuna an fusata ‘yan ta’addan ne saboda sojoji sun hana a aiko masu da kudin fansa
  • Wasu ‘yanuwan wadanda ke tsare sun yi niyyar biyar kudin fansa, amma jami’an tsaro suka hana

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Bayanai suna kara fitowa a game da bidiyon da aka fitar a karshen makon jiya, inda aka ga ana dukar fasinjojin jirgin da aka yi garkuwa da su.

Daily Trust a rahoton da ta fitar a ranar Litinin 25 ga watan Yuli 2022, ta ce hakan ya biyo bayan matsalar da aka samu wajen aikawa ‘yan ta’addan kudi.

An samu cikas ne a yunkurin da ‘yan ta’addan suka yi na karbar kudin fansa domin fito da wasu daga cikin wadannan Bayin Allah da ke tsare a hannunsu.

Kara karanta wannan

2023: Sanusi II ya yi Jawabi a Game da Zabe, ya Bayyana cikas 1 da ake Fuskanta

Ana tattaunawa da ‘yan ta’addan, kuma har an yi niyyar za a saki wasu mutanen da nufin ‘yanuwa za su biya kudin fansa, sai jami’an tsaro suka hana a biya.

Ran 'yan ta'adda ya baci

Jaridar ta ce wannan abin da jami’an tsaro suka yi ya fusata ‘yan ta’addan. A dalilin haka ne aka fitar da bidiyo ana ta dukansu, tare da yi masu barazana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani daga cikinsu da ya yi jawabi a faifen bidiyon, ya zargi gwamnati da yi wa kwamitin tattaunawar karya da neman hanyar ceto mutanen da karfi.

Jirgin Kaduna-Abuja
Jirgin kasan Kaduna-Abuja da aka kai wa hari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Mukhtar Shuaibu ya tabbatar da cewa miyagun da ke tsare da su, ba su ji dadin yadda dakarun sojoji suka hana biyan kudin fansa, bayan an gama magana ba.

Kamar yadda jaridar ta fitar da rahoto, wasu da ‘danuwansu ke rashin lafiya a tsare sun yi niyyar biyan kudi domin a fanshe shi, amma sai sojoji suka hana.

Kara karanta wannan

Bayan Kuje, ‘Yan ta’adda na Tsara Yadda za su Shiga Wasu Kurkuku 3 a Jihohin Arewa

Sojoji za su kama masu biyan fansa

Da ‘yanuwan suka je inda za a hadu da ‘yan bindigan a cikin wani jeji, sai suka ci karo da jami’an tsaro. Abin ya kai sojojin sun yi barazanar za su cafke su.

Sojojin sun fadawa masu neman biyan kudin cewa bada fansa ya sabawa doka, don haka za su kama su. Majiyar tace wannan ne ya batawa ‘yan ta’addan rai.

Ganin watanni hudu kenan gwamnatin kasar ta gagaro ceto su, wasu ‘yanuwan wadannan mutane sun saida kadarorinsu domin kubutar da masoyansu.

Za a fasa gidajen yari

Dazu kun ji labari cewa an ankarar da hukumar da ke kula da gidajen gyaran hali na kasa cewa za a iya shiga kurkukun jihohin Zamfara, Kebbi da Katsina

A karshen mako ne ‘yan ‘ta’addan suke sa ran su rika kai hari. Hakan ya biyo bayan fasa gidan kurkukun Kuje da aka yi a birnin tarayya, aka tsere da mutane.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun tari motar gwamnati, sun sheke direba, sun sace fasinjoji sama da 30

Asali: Legit.ng

Online view pixel