Kanwar Gwamnan Gombe, Hajiya Aisha Yahaya, Ta Rasu, Shugaba Buhari YA Yi Ta'aziyya
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi wa gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ta'aziyar rasuwar ƙanwarsa
- Buhari, wanda ya nuna damuwarsa, ya ce mutane zasu jima suna tuna ɗumbin alkairin da ta yi a lokacin rayuwarta
- Hajiya Aishatu Yahaya Umaru, ta rasu da safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, 2022 bayan fama da jinya
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jajantawa gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe, bisa rasuwar ƙanwarsa, Hajiya Aisha Yahaya Umaru.
Shugaban ya aike da sakon ta'aziyyarsa ga gwamnan ne a wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Buhari ya ce Marigayya Hajiya Aishatu, ta ba da gudummuwa mara misaltuwa wajen kyautawa da tallafa wa al'ummar yankinsa wanda zai sa mutane da dama ba zasu mance da ita ba.
Shugaban ƙasan ya ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Na shiga jimami da jin rasuwarta, Addu'a ta na tare da iyalanta, ɗan uwanta, mai girman gwamna da ɗaukacin al'ummar jihar Gombe. Allah ya karɓi baƙuncinta kuma ya saka mata bisa kyawawan ayyukanta."
Yaushe gwamnan ya yi wannan babban rashi?
Yar kimanin shekara 48, Hajiya Aishatu, ta rasu ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli, 2022 a Gombe bayan fama da rashin lafiya.
Tribune ta rahoto a Wata sanarwa da Ofishin mai girma gwamna ya fitar, ta bayyana cewa:
"Inna Lillahi Wa Inna lillahi Rajiun, tare da miƙa lamarin mu ga Allah SWA, iyalan marigayi Alhaji Yahaya Umaru, na baƙin cikin sanar da rasuwar yar uwar mu da muke kauna, Hajiya Aishatu, wacce ta rasu bayan fama da jinya."
A wani labarin kuma DCP Abba Kayri ya sake neman beli a Kotu, ya ce kamar Ɓera haka ya ɓuya lokacin harin yan ta'adda a gidan Yarin Kuje
Abba Kyari, dakataccen mataimakin kwamishinan yan sanda, ya ce ya ɓuya kamar ɓera lokacin harin yan ta'adda a Kuje.
A zaman Kotu na yau Laraba, Kyari ta bakin lauyansa ya sake shigar da bukatar beli, ya ce ya samu damar tsere wa amma ya ƙi.
Asali: Legit.ng