Tashin hankali, Jami'an tsaro sun buɗe wa yan zuwa ɗaura aure wuta, sun kashe da yawa

Tashin hankali, Jami'an tsaro sun buɗe wa yan zuwa ɗaura aure wuta, sun kashe da yawa

  • An shiga yanayin tashin hankali yayin da wasu yan bindiga da ake zaton jami'an tsaro ne suna ƙashe mutum 7 a hanyar komawa gida a Imo
  • Wani shugaban ƙauyen da mutanen suka fito ya ce yanzu haka wasu na kwance a Asibiti rai hannun Allah wasu kuma an sallame su
  • Mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar Imo, Michael Abattam, ya ce tuni hukumar su ta fara bincike

Imo - Mutane sun shiga tashin hankali da ruɗani yayin da wasu yan bindiga da ake tsammanin jami'an tsaron Ebubeagu da aka kafa a kudu maso gabas ne suka halaka baƙin ɗaura aure 7.

The Nation ta ruwaito cewa lamarin wanda ya faru ranar Lahadi ya jefa tashin hankali a cikin zuƙatan mazauna jihar Imo.

Bayanai sun nuna cewa mutanen na kan hanyar komawa ƙauyen Otulu, ƙaramar hukumar Oru ta gabas daga ƙauyen Awomama da suka je biki kafin yam bindigan su buɗe musu wuta.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari jihar shugaban ƙasa ana ruwan sama, sun aikata ɓarna

An samu matsala a jihar Imo.
Tashin hankali, Jami'an tsaro sun buɗe wa yan zuwa ɗaura aure wuta, sun kashe da yawa Hoto: thenationonline
Asali: Twitter

Shugaban ƙauyen Otulu, Nnamdi Agbor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, ya ce mutum Bakwai ne suka mutu nan take.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Mutanen mu na kan hanyar dawowa daga Awo Omamma da kusan karfe 7:00 na dare bayan sun halarci ɗaura auren gargajiya, Yayin da dakarun Ebubeagu suka hange su sai suka buɗe musu wuta."
"A yanzu da nake muku magana mun gano gawarwakin mutum 7 waɗan da mutanen mu ne, biyar sun ɓata, biyu na kwance rai hannun Allah yayin da sauran da suka ji raunuka kaɗan an sallame su."
"Abun takaici ne, mutanen mu sun fusata sun fara zanga-zanga, ba dalilin wannan kisan. Suna kan hanyar zuwa gida lokacin da jami'an suka buɗe musu wuta. Haka ba ta taɓa faruwa ba a baya."

Wane mataki suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Gwamna ya sallami baki ɗaya hadimansa daga kan kujerunsu saboda abu ɗaya

Shugaban ƙauyen ya ƙara da cewa ya kai rahoton abinda ya faru da jami'an tsaro, ya gaya wa kwamishinan yan sanda, kwamandan sojoji da DPO na yankin wanda yana iya kokarinsa.

Bugu da ƙari, Nnamdi Agbor, ya ce ya gaya wa ɗan majalisa mai wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Imo, kamar yadda daily trust ta ruwaito.

Da aka tuntuɓe shi, mai magana da yawun hukumar yan sanda reshen jihar Imo, Micheal Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ƙara da cewa tuni aka fara bincike.

A wani labarin kuma 'Yan bindiga sun sake kai hari kusa da makarantar Sojoji NDA a Kaduna

Bayanai sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da mai juna biyu da wasu mutane Bakwai a harin wanda suka shiga gida-gida.

Kakakin hukumar yan sandan Kaduna ya ce ba shi da masaniya amma zai bincika kafin ya yi magana a kai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun sake kai hari kusa da makarantar Sojoji NDA a Kaduna

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel