'Yan bindiga sun sake kai hari Dutsin-ma, sun sace matan aure da kananan yara

'Yan bindiga sun sake kai hari Dutsin-ma, sun sace matan aure da kananan yara

  • Makonni kaɗan bayan kashe kwamandan yankin Dutsinma, yan bindiga sun yi garkuwa da mutum Tara a Shema Quaters
  • Maharan sun yi awon gaba da matan aure hudu da kananan yara biyar a harin da suka kai cikin garin Dutsinma ana tsaka da ruwa
  • Kakakin yan sandan jihar ya ce tuni hukumar su ta ƙara jibge dakaru kuma sun baza komar su don ceto mutanen

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - 'Yan bindiga da ake zaton yan fashin daji ne sun yi garkuwa da mutum Tara, matan aure hudu da kananan yara biyar a yankin Shema Quarters cikin ƙaramar hukumar Dutsinma, jihar Katsina.

Daily Trust ta ce wannan harin na zuwa ne makonni kaɗan bayan kashe kwamandan yanki na Dutsinma, mataimakin kwamishinan yan sanda, ACP Aminu Umar, wanda yan bindigan ke kira, 'Mai ceton Dutsin-Ma'.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun sace wani babban Basarake a arewa

Yan bindiga sun kai hari Dutsinma.
'Yan bindiga sun sake kai hari Dutsin-ma, sun sace matan aure da kananan yara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan fashin da adadi mai yawa sun mamaye Anguwar Shema Quarters da ke cikin garin Dutsin-Ma da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Lahadi.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun shafe mintuna 30 suna aikata ta'asa kafin wasu jami'an tsaro su kawo ɗauki yankin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mazaunin Anguwar wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya shaida wa wakilin jaridar cewa wannan ne karo na farko da yan fashin dajin suka kai farmaki yankin.

Mutumin ya ce:

"Lokacin ana ruwa,wani maƙocin mu ya kira ni a waya ya faɗamun cewa yan bindiga na kokarin buɗe kofar gidan maƙoci Abdulaziz Lawal da tsiya kuma ba abun da zamu iya yi saboda suna harbi."
"Bayan sun kutsa kai gidan, sun tafi da matar aure da ɗan jaririnta da wata matar auren ta daban tare da kanwarta. Daga nan suka kutsa gidan Usman Datti Yarima, suka ɗauki matansa biyu da yara uku, jumulla mutum Tara kenan."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Jami'an tsaro sun buɗe wa baƙin ɗaura aure wuta, sun kashe da dama

Ya kara da cewa dukka Magidantan biyu na nan cikin gidajensu lokacin da maharan suka shiga, ɗaya ya tsallake katanga yayin da ɗayan kuma ya ɓuya a Cilin.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntuɓe shi, kakakin hukumar yan sanda reshen jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa an sace mutum Tara.

Ya ce tuni jami'an yan sanda suka bazama neman inda maharan suka yi domin ceto mutanen cikin ƙoshin lafiya, kuma an ƙara yawan dakaru a yankin.

Wani mazaunin Shema Quaters, ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa tabbatas ranar sun kwana cikin ɗar-ɗar da tashin hankali bayan harin yan bindigan.

Mutumin wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya shaida mana cewa maharan sun shigo da harbe-harbe, kuma suka shiga gidajen mutum biyu. A cewarsa sun ji karar harbi daga ɓangaren yamma.

Ya ce:

"Ɓarayi ne waɗan da ake cewa yan bindiga suka shigo da ƙarfe 11:50 na dare, suka shiga gidan Usman Yarima a rukunin gidaje O, suka ɗauke matan aure da yara, cikin matan har da mai ciki, haihuwa yanzu ko anjima." inji shi.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An cafke wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna

Ya ƙara da cewa bayan nan suka sake shiga wani gida suka ɗauki mata da ƙanwatar, tun da suka shigo ba su bar Anguwar ba har ƙarfe 3:00 na dare, gab da Asuba.

Mutumin ya shaida wa wakilin Legit.Hausa cewa maharan sun kira iyalan waɗan da suka sace suka sanar musu cewa sun isa maɓoyar su lafiya.

A wani labarin kuma, Gwamnati a maƙociyar jihar Katsina wato Kano ta haramta amfani da Adaidaita Sahu bayan karfe 10:00 na dare a faɗin jihar

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagoncin gwamna Abdullahi Ganduje ta hana 'yan Adaidaita sahu aiki bayan ƙarfe 10:00 na dare, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sabuwar dokar na ƙunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano , Malam Muhammad Garba ya fitar ranar Litinin, ya ce dokar zata fara aiki ne ranar Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel