Bidiyo: Fusatattun jama'a sun yi wa matashi tumɓur bayan an kama shi yana satar ɗan kamfan mata

Bidiyo: Fusatattun jama'a sun yi wa matashi tumɓur bayan an kama shi yana satar ɗan kamfan mata

  • Dubun wani matashi ta cika bayan da aka kama shi dumu-dumu yana kokarin satar 'dan kamfan mata a igiyar shanya
  • Fusatattun jama'a sun taru tare da yi masa tumbur bayan kama shi da suka yi a yankin Akenfa dake Yenagoa a jihar Bayelsa
  • An gano cewa, matashin yayi ikirarin cewa ya je ziyartar wata 'yar uwarsa ne dake yankin da asussuba na ranar Juma'a da ta gabata

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yenagoa, Bayelsa - Fusatattun jama'a sun yi wa wani matashi tumbur haihuwar uwarshi a jihar Bayelsa bayan sun kama shi yana yunkurin satar 'dan kamfan mata.

An tattaro cewa, lamarin ya faru ne a yankin Akenfa dake karamar hukumar Yenagoa ta jihar Bayelsa dake kudancin Najeriya a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 15 ga watan Yulin 2020.

Taswirar jihar Bayelsa
Bidiyo: Fusatattun jama'a sun yi wa matashi tumɓur bayan an kama shi yana satar ɗan kamfan mata. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A bidiyon da ThisisBayelsa suka fitar, wanda ake zargin yayi ikirarin cewa ya ziyarci 'yar uwarshi mai suna Blessing.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An cafke wani dan shekara 60 da ya tsere daga gidan yarin Kuje a Kaduna

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bidiyon, an ga matashin ya ci mugun duka a hannun jama'a sannan suna tambayarsa abinda ya je yi a gidan da wannan sanyin safiya.

An ji barawon 'dan kamfan yana cewa, "Wurin 'yar uwata naje, tana zama a gidan."

Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida

A wani labari na daban, magidanci mai shekaru 55 ya sheke matarsa mai shekaru 45 bayan ya zargeta da cin amanarsa kuma daga bisani yayi tafiyar kusan kilomita 12 zuwa ofishin 'yan sanda da kanta.

Lamarin ya faru ne a Chandrasekharpur dake yankin Odisha Dhenkanal a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 15 ga watan Yulin 2022.

Bidiyon mai matukar ban tsoro na mutumin yana tafe da kan matarsa da ya sheke ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

Kara karanta wannan

ASUU: Hotunan dalibin da ya bude gidan cin abinci, shi ke girkawa kuma yake siyarwa

'Yan sanda sun kama wanda ake zargin yayin da yake tafe da cirarren kanta zuwa ofishin 'yan sanda dake yankin Dhenkanal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel