Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida

Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida

  • Magidanci mai shekaru 55 a duniya ya sheke matarsa sakamakon zarginta da yake yi da neman maza a waje bayan tana da aurensa a kanta
  • Ya tashi a daren Juma'a inda ya halaka matarsa wacce suka kwashe tsawon shekaru 25 da aure sannan ya kama hanya ya kai kansa ofishin 'yan sanda da kanta da ya cire
  • A kan hanyarsa ta zuwa ne wasu 'yan sandan suka kama shi tare da kwace muguwar wukar dake hannunsa wacce da ita yayi aika-aikar.

Magidanci mai shekaru 55 ya sheke matarsa mai shekaru 45 bayan ya zargeta da cin amanarsa kuma daga bisani yayi tafiyar kusan kilomita 12 zuwa ofishin 'yan sanda da kanta.

Lamarin ya faru ne a Chandrasekharpur dake yankin Odisha Dhenkanal a sa'o'in farko na ranar Juma'a, 15 ga watan Yulin 2022.

Kara karanta wannan

Fashin magarƙama: An kama wani fursuna da ya tsere daga gidan Yarin Kuje ɗauke da kayan laifi a Katsina

Magidanci
Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Bidiyon mai matukar ban tsoro na mutumin yana tafe da kan matarsa da ya sheke ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

'Yan sanda sun kama wanda ake zargin yayin da yake tafe da cirarren kanta zuwa ofishin 'yan sanda dake yankin Dhenkanal.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wanda ake zargin mai suna Nakaphodi Majhi, 'dan asalin kauyen Chandrasekharpur ne kuma ya aura matarsa mai suna Sachala Majhi shekaru 25 da suka gabata.

Suna da 'ya'ya biyu wadanda ke rayuwa a wajen kauyen.

Wani 'dan sanda a Nakaphodi yace wanda ake zargin yana zargin Sachala ne da cin amanarsa kuma a kodayaushe yana takalarta fada.

Bayan fadace-fadace a tsakanin ma'auratan, kusan kullum basu zaman lafiya.

Wurin karfe 3:30 na dare zuwa 4 na safiyar Juma'a, Nakaphodi ya halakata ta hanyar yanka makogwaronta da makami mai kaifi da ake kira da Katuri.

Kara karanta wannan

Wankan sallah: Hadadden hoton gwamnan Zamfara, Bello Matawalle da yaransa maza

Daga nan ya cire kanta kuma ya isa ofishin 'yan sandan Gondia da cirarren kanta tare da mikawa 'yan sanda, 'dan sandan yace.

A kan hanyar sa ta zuwa, wasu mutane sun kama shi a kauyen Jankira karkashin Joranda kuma suka sanarwa 'yan sandan Joranda lamarin.

Bayan samun labarin, 'yan sandan sun garzaya tare da cafke wanda ake zargin. Sun kwace makamin da ke hannunsa tare da kan matarsa.

Ana cigaba da bincike kan lamarin a halin yanzu.

Magidanci
Zargin cin amana: Hotunan magidanci da ya sheke matarsa, ya mika kansa hannun 'yan sanda da muhimmiyar shaida. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Bidiyo: Yadda jama'a suka kama kada, zasu farke cikinta don ceto yaron da ta hadiye

A wani labari na daban, wasu fusatattun mazauna kauyen Raghunathpur, yankin Madhya Pradesh Sheopur dake Indiya sun cafke kada domin yanka cikinta su fito da yaro 'dan shekaru bakwai da ta hadiye da ran shi.

Kadar ta kai wa yaron mai suna Antar Singh farmaki lokacin da yake wanka a kogin Chambal a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli kuma ta ja shi har cikin kogin.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Sadiq Ango ya canza kamanni bayan yin wata 3 hannun 'yan bindiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel