Yan bindiga sun kai wa masaukin masu bautan kasa hari a Akwa Ibom

Yan bindiga sun kai wa masaukin masu bautan kasa hari a Akwa Ibom

  • Yan bindiga sun yiwa masu bautan kasa fashi a masaukin na jihar Akwa Ibom a daren ranar Laraba
  • Hukumar kula da bautan kasa ta jihar Akwa Ibom ta ce babu wanda aka yiwa fyade a lokacin da take tabbatar da harin da aka kai wa yan NYSC a jihar
  • Kwamishinan yansandar Jihar Akwa Ibom ya ba da tabbacin bincike da kama masu laifin nan ba da jimawa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Akwa Ibom - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari a wani masauki da wasu masu yi wa kasa hidima (NYSC) ke zaune a jihar Akwa Ibom. Rahoton Channels TV

An tattaro cewa ‘yan bindigar da misalin karfe 1:00 na ranar Laraba, sun kai hari tare da kwace kayayyakin masu daraja a layin Udo Ekong Ekwere Street dake, Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An nemi Abba Kyari, Dariye, Nyame an rasa a magarkamar Kuje a harin 'yan bindiga

Wani da abun ya faru a gaban shi yace masu bautan kasa 21 ne aka yiwa fashi a masaukin su.

Yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, Hukumar Kula da NYSC na jihar, ta ce sabanin rahotannin da ake samu a wasu kafofi, babu wanda aka yi wa fyade.

nysce
Yan bindiga sun kai wa masaukin masu bautan kasa hari a Akwa Ibom
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, Ko’odinetan NYSC na jihar, Misis Chinyere Ekwe ta ce ita da kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Olatoye Durosinmi, sun ziyarci wurin domin tantance ainihin abun da ya faru.

A lokacin da take wurin, an tabbatar da yan NYSC 21 aka yiwa fashi a masaukin su. Tattaunawar da tayi da su ya kara nuna cewa barayi ne suka kai musu hari da misalin karfe 1 na safiyar yau.

“A cikin haka ne maharan suka kwashe kayansu masu daraja da suka hada da wayoyi, Laptop da wasu kudade. Sun tabbatar da cewa ba a yi musu lahani a jikinsu ba, kuma babu yan bautar kasar da da aka yi wa fyade,” Misis Ekwe ta bayyana.

Kara karanta wannan

Hukumar Kula da Gidan kason Kuje tace an kwantar da kuran

Sai dai Misis Ekwe ta bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya baiwa jami’an hukumar da sauran jama’a tabbacin cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin kuma nan ba da jimawa ba za a cafke masu laifin.

Duk da makudan kudin da ake kashewa an kasa samun tsaro a Najeriya

Jihar Katsina - Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam a katsina sun yi kira ga gwamnatin tarayya ta musu bayani akan makudan kudaden da ake kashewa a harkar tsaro dan ganin an kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Rahoton jaridar PUNCH.

Kungiyoyin sun yi wannan kiran ne a ranar Talata da suke tsokaci akan kisan babban Dansandan ACP Aminu Umar, da yan bindiga suka kashe a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel