Majalisar Malaman Jihar Oyo ta ba wa Ganduje sarautar Mai Addini na kasar Yarbawa

Majalisar Malaman Jihar Oyo ta ba wa Ganduje sarautar Mai Addini na kasar Yarbawa

  • Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu sabuwar sarautar mai riko da addini na kasar Yarbawa karshen makon da ya gabata
  • Wannan ya biyo bayan nadin sarautar da Olubadan of Ibadan ya masa na Aare Fiwajoye na kasar Ibadan
  • Gwamna Ganduje suruki ne ga tsohon gwamnan jihar Oyo, Marigayi Abiola Ajimobi

Ibadan - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu mukamin Alaadini na kasar Yarbawa daga wajen Majalisar Malaman kasar Oyo, Kudu maso yammacin Najeriya.

Kasar Oyo ce cibiyar daular mulki na yankin Yarabawa.

Mukamin Alaadini na nufin mai riko da addini.

Hadimin Gwamna Ganduje na hotuna, Aminu Dahiru, ya fitar da jawabi da hotunan kan wannan nadi da akayiwa Ganduje, a cewarsa:

"A ranar Asabar 18 ga watan Yuni ne Majalisar malamai ta yankin jihohin yarabawa wanda suke da cibiya a Ibadan Babban birnin jihar Oyo suka baiwa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Sarautar ALAUDDEN OF YORUBAWA (ALADDIN OF YORUBA) Karkashin Jagorancin Shugaban majalisar limamai da malamai na Jihar Oyo, Sheikh Abdulganiyy Abubakar (AGBOLOMOKEKERE)."

Kara karanta wannan

APC ta nada Ganduje shugaban yakin neman zaben Gwamnan jihar Osun

Shugaban majalisar malaman, Sheikh Abdulganiyy Abubakar, ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ana bada sarautar ne kadai ga Musulmi mai riko da addini da kuma yiwa addinin hidima inda binciken su ta tabbatar musu da cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje shine ya cika wannan sharudan ya kuma taya shi murna bisa hakan."

Kalli hotunan:

Alaadin
Majalisar Malaman Jihar Oyo ta ba wa Ganduje sarautar Mai Addini na kasar Yarbawa Hoto: Aminu Dahiru
Asali: Facebook

Nadin Ganduje
Majalisar Malaman Jihar Oyo ta ba wa Ganduje sarautar Mai Addini na kasar Yarbawa Hoto: Aminu Dahiru
Asali: Facebook

Ganduje
Majalisar Malaman Jihar Oyo ta ba wa Ganduje sarautar Mai Addini na kasar Yarbawa Hoto: Aminu Dahiru
Asali: Facebook

An yiwa Gwamna Ganduje da Gwaggo nadin sarauta a garin Ibadan

An yiwa Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, nadin sarautan 'Aare Fiwajoye' na garin Ibadan yayinda za'a yiwa uwargidarsa, Hajiya Hafsat, nadin Yeye Aare Fiwajoye.

Sarki (Olubadan) na garin Ibadan ne ya yiwa gwamnan nadin ranar Asabar, 18 ga watan Yuni, 2022.

Mai magana da yawun Sarkin Ibadan, Oladele Ogunsola, ya bayyana cewa za'a yiwa Ganduje nadin ne bisa shawarar Sarkin Yarbawa mazauna jihar Kano, Alhaji Murtala Alimi Otisese (Adetimirin-1).

Asali: Legit.ng

Online view pixel