Bayan kwanaki 85, Buhari ya ce lokacin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya yi

Bayan kwanaki 85, Buhari ya ce lokacin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya yi

  • Bayan rahoton cewa macizai sun cijesu, Buhari ya umurci jami'an tsaro su ceto maza, mata da yara 50
  • Shugaban kasan ya ce lokacin cetosu yayi bayan sun kwashe kimanin watanni uku hannun yan bindiga
  • Yan bindiga sun bayyanawa gwamnati cewa ba kudi suke bukata, musanyan fursunoni suke so

Bayan kwanaki 85 da sacesu a harin jirgin kasan Abuja/Kaduna, Shugaba Muhammau Buhari ya umurci jami'an tsaro su ceto sama da mutum 50 da suka rage hannun yan bindiga.

Legit ta kawo muku cewa a ranar 28 ga Maris, 2022, wasu yan bindiga sun kai farmaki jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna inda suka hallaka akalla mutum 8, suka jikkata goma kuma sukayi awon gaba da mutum 62.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga: Mun Fara Kare Kanmu A Birnin Gwari, In Ji Shugaban Al'umma a Kaduna

Bayan kimanin watanni uku, Shugaba Buhari ya bayyana cewa wajibi ne a ceto wadanda ke hannun yan bindiga da ransu.

Ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Tuwita.

Yace:

"Na umurci hukumomin tsaro da na leken asiri ta gaggauta ceto sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna cikin koshin lafiya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Umurni daya shine wajibi ne a cetosu gaba baya da rai, cikin gaggawa."
"Ba zamu yi kasa a gwiwa ba sai an ceto dukkan sauran."
Buhari
Bayan kwanaki 85, Buhari ya ce lokacin ceto fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya yi Hoto: Presidency
Asali: Instagram

Jagoran Sasanci Da 'Yan Bindiga Ya Janye, Ya Sanar Da Mawuyacin Halin Da Fasinjojin Ke Ciki

Ragowar fasinjoji 50 da aka sace a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suna fuskantar barazanar cizon macizai da ciwuka masu matukar illa ga rayukansu.

Mallam Tukur Mamu, wanda shi ne ke jagorantar sasancin tsakanin gwamnatin tarayya da 'yan bindigan ya bayyana hakan a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai sabon kazamin hari Kaduna, sun kashe jami'an tsaro sun sace dandazon mutane

Rahoton Punch ya bayyana cewa 'yan bindigan sun sako mutum 11 daga cikin 61 dake hannunsu bayan kwashe kusan watanni uku a hannun 'yan ta'addan.

Mamu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kokari wurin ceto sauran fasinjoji 50 da ke hannun 'yan ta'addan kafin lokaci ya kure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel