Kana zuwa Turai da iyalanka amma ka hanamu zuwa: Alkalan kotun koli sun kalubalanci Shugaban Alkalai

Kana zuwa Turai da iyalanka amma ka hanamu zuwa: Alkalan kotun koli sun kalubalanci Shugaban Alkalai

  • Alkalan kotun koli sun kalubalanci Shugaban Alkalan Najeriya kana hana su abubuwa jin dadi amma shi yana shakatawarsa
  • Alkalan sun ce sau biyu kadai suka je Dubai da Zanzibar a shekarar nan sabanin yadda aka saba
  • Sun bukaci Alkali Tanko Mohammed yayi bayanin yadda aka yi da kudaden da kotun ke samu

Abuja - Alkalan kotun kolin Najeriya sun aikewa Alkalan Alkalai, Ibrahim Tanko Mohammed wasikar kar ta kwana bisa abubuwan dake gudana a babbar kotun Najeriya.

A wasikar da manema labarai suka gani, Alkalan kotun koli 14 sun tuhumci Alkali Tanko Mohammed da gazawa wajen gudanar da ayyukansa matsayin shugaba.

Tanko
Kana zuwa Turai da iyalanka amma ka hanamu zuwa: Alkalan kotun koli sun kalubalanci Shugaban Alkalai Hoto: Presidency
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon Alkalin Alkalai zai tashi da Naira Biliyan 2.5 bayan ya yi murabus daga ofis

Abubuwan da Alkalan suka lissafa a wasikar sun hada da gidaje, motoci, lantarki, man Gas, yanar gizo a gidajen Alkalai, horo, da rashin wuta a kotuna.

A wasikar, Alkalan suka ce:

"Mun aike maka wannan wasika tun ranar 24 ga Maris 2022, amma kayi uwar watsi da ita."
"A baya a kan tura Alkalai waksho da horo sau biyu zuwa uku a shekara tare da abokin rakiya."
"Amma tun lokacin da ka shiga Ofis, sau biyu kadai Alkalai suka halarci waksho a Dubai da Zanzibar. Ko abokan rakiya ba'a bamu ba."
"Gaba daya ka yi watsu da mu amma kai kana yawo duniya da matarka, yaranka da hadiminka."
"Muna bukatar sanin halin da kudaden suke, shin an karkatar da su ne, ko kawai an hana mu ne?"

Asali: Legit.ng

Online view pixel