Tsohon Alkalin Alkalai zai tashi da Naira Biliyan 2.5 bayan ya yi murabus daga ofis

Tsohon Alkalin Alkalai zai tashi da Naira Biliyan 2.5 bayan ya yi murabus daga ofis

  • Tanko Ibrahim Muhammad zai iya samun kudin da sun haura Naira Biliyan 2 bayan ajiye aikinsa
  • A dokar Najeriya, an ware makudan kudin sallaman da ake biyan duk wani Alkalin Alkalai na kasa
  • Baya ga kudin sallama da fansho da Tanko Ibrahim Muhammad zai karba, za a dankara masa gida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ana sa rai tsohon Alkalin Alkalai na kasa, Tanko Ibrahim Muhammad zai samu Naira biliyan 2.5 daga hannun gwamnatin tarayya bayan ajiye aiki.

The Punch ta kawo rahoto a makon nan cewa kamar yadda aka saba a al’ada, akwai kudin da gwamnatin tarayya ta ke warewa shugaban Alkalai na Najeriya.

Bayan Muhammadu Buhari ya nada Mai shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin babban Alkalin kasa, ana tsammani wanda ya bar kujerar zai samu kudin sallama.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa zata binciki Alkalin Alkalai da yayi murabus, Tanko Mohammad, bisa zargin rashawa

Kamar yadda majalisar shari’a ta kasa watau NJC tayi tanadi, Alkalin Alkalai zai samu katafaren gida da za a gina masa a garin Abuja ko duk inda yake sha’awa.

Baya ga haka, gwamnatin tarayya za ta dauki dawainiyar gyara wannan gida da kayan daki.

Akwai miliyoyi na kudin sallama

Rahoton ya ce bugu da kari, tsohon Alkalin Alkalan zai karbi kudin sallama wanda ya kai 300% na albashin shekara, sannan za a rika biyansa fansho har abada.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tanko Mohammed
Tsohon Alkalin Alkalai na kasa, Tanko Mohammed
Asali: Facebook

Albashin da yake karba a lokacin yana ofis na tsawon shekara daya ya haura Naira miliyan uku.

Haka aka saba a dokar kasa

Majalisar shari’ar ta bukaci a biya Mai shari’a Walter Onnoghen irin wannan kudi a lokacin da ya ajiye aiki a 2019. Bayan ya yi murabus ne Tanko ya zama CJN.

Legit.ng Hausa ta fahimci sauran Alkalin Alkalan da aka yi a baya, sun samu wannan dama. Irinsu Salihu Modibbo Belgore sun tabbatar da an gina masu gida.

Kara karanta wannan

Kotu ta ki Sauraron Shari'o'in Lauyan da Yayi Shigar Bokaye Zuwa Kotu

Wata sabuwa a Majalisa

Ana maganar kudin da Tanko Mohammed zai samu ne kuma sai rahoto ya zo cewa kwamitin shari’a da kare hakkin Bil Adama a majalisa zai bincike shi.

Shugaban majalisar dattawa na kasa, Ahmad Lawan ya umarci wannan kwamiti ya yi bincike a kan korafin da Alkalan kotun koli su ka rika yi a kan Tanko.

Sanata Ahmad Lawan ya ce majalisa za ta yi wannan bincike domin ganin yadda za ta kawo gyara duk da wanda ake tuhuma ya bar ofis a halin yanzu.

Ya aka yi CJN ya bar aiki?

Kun samu rahoto a makon nan cewa ana tunanin matsalar rashin lafiya ne ya jawo Mai shari'a Tanko Muhammad ya sauka daga babbar kujerar da yake kai.

Alkalin Alkalan ya rubuta takardar murabus, wannan mataki da ya dauka ya ba mutane mamaki. Amma ana zargin cewa rashin lafiya ta tursasa masa yin ritaya.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel