Kano: Gwamna Ganduje ya Nada 'Dan-Agundi Mukaddashin Manajan Daraktan KSCPC

Kano: Gwamna Ganduje ya Nada 'Dan-Agundi Mukaddashin Manajan Daraktan KSCPC

  • Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya amince da nada Baffa Babba Dan-Agundi a matsayin mukaddashin manajan daraktan hukumar kula da kayayyakin siyarwa na Kano
  • A cewar sakataran yada labaran gwamna, an nada Dambazau, wanda a halin yanzu shi ne daraktan kungiyar KAROTA na wucin gadi kafin a nada sabon manajan daraktan dindindin
  • Dan Agundi a halin yanzu shine shugaban hukumar kula da lamurran kan titunan jihar Kano, Karota

Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya amince da nada Baffa Babba Dan-Agundi a matsayin mukaddashin Manajan Daraktan na Hukumar kula da kayyakin siyarwa na Kano (KSCPC).

Hakan ya bayyana ne a wata takarda da babban sakataran yada labaran gwamna, Abba Anwar ya fitar a ranar Litinin a Kano.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Najeriya ta kuduri kawar da amfani da kananzir nan da 2030

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Kano: Gwamna Ganduje ya Nada 'Dan-Agundi Mukaddashin Manajan Daraktan KSCPC. Hoto daga solacebase.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Anwar ya ce nadin ya fara aiki ne tun daga lokacin da Manajan Daraktan ya ajiye aikinsa.

"A matsayinsa na MD rikon kwarya, zai lura da dukkan al'amuran hukumar, daga na aiki har da sauransu, da sa ran daidaita komai yadda ya dace, kafin a nada manaja na dindindin," a cewarsa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito yadda aka nada Dan-Agundi a matsayin daraktan hukumar kula da lamurran kan titi na Kano (KAROTA) a baya.

NAN ta ruwaito yadda manajan daraktan KSCPC, janar Idris Bello Dambazau (mai ritaya) ya ajiye aikinsa da kansa babu gaira babu dalili.

Gwamnan Kano ya nada sabbin kwamishinoni uku

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya aika wa Majalisar Jihar sunayen kwamishinoni uku da ya zaba domin samun amincewar majalisar.

Kara karanta wannan

Allah Yayi wa Dr Ahmad Yakasai, MD na HML din 'Yan Sandan Najeriya, Rasuwa

Kakakin Majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a ranar Talata a Kano kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Gafasa ya ce gwamnan na neman amincewar majalisar domin nada Idris Garba a matsayin kwamishina kuma mamba na Majalisar Zartarwa na Jihar, SEC.

Ya ce gwamnan ya kuma nemi yan majalisar su tabbatar da nadin wasu kwamishinoni biyu a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na jihar, KANSIEC. A cewarsa, ana sa ran Garba zai bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba domin a tantance shi.

Ya bukaci wanda zai zo tantancewar kada ya taho da yan rakiya fiye da biyar don bin dokokin kare yaduwar COVID-19.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng