Allah Yayi wa Dr Ahmad Yakasai, MD na HML din 'Yan Sandan Najeriya, Rasuwa

Allah Yayi wa Dr Ahmad Yakasai, MD na HML din 'Yan Sandan Najeriya, Rasuwa

  • Dr. Ahmad Garba Yakasai, manajan daraktan Cibiyar Gudanarwa ta Kiwon Lafiya ta 'Yan sandan Najeriya, ya rasu
  • Gogaggen likitan 'dan asalin jihar Kano mai sama da shekaru 20 na gogewa, ya rasu sakamakon mummunan hatsarin mota da yayi
  • Ya rasu a ranar Asabar kuma an yi jana'izarsa tare da birne shi a garin Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a ranar Lahadi

Allah ya yi wa Dr. Ahmad Garba Yakasai, manajan daraktan Cibiyar Gudanarwa ta Kiwon Lafiya ta 'Yan sandan Najeriya, rasuwa.

Kwararren likitan 'dan asalin jihar Kano, ya rasu ne sakamakon mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi a babban titin Damaturu, jihar Yobe.

Ya rasu a ranar Asabar, 18 ga watan Yunin 2022 kuma na yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a cikin garin Kano wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

Dole Bola Tinubu Ya Fada Wa Yan Najeriya Yadda Ya Tara Dukiyarsa, In Ji Deji Adeyanju

Dr Ahmad Garba Yakasai, MD/CEO na HMO na 'Yan Sandan Najeriya
Allah Yayi wa Dr Ahmad Yakasai, MD na HMO din 'Yan Sandan Najeriya, Rasuwa
Asali: Original

Fitaccen likitan ya kasance kwararre a fannin da ya shafin matsalolin mata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Likitan wanda ke da gogewar aiki na sama da shekaru 20, ya bayar da gudumawa mai tarin yawa a fannin lafiya.

Ya samu digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Bayan nan, ya samu digiri na biyu a fannin ilimin tattalin arziki a fannin lafiya a jami'ar Bayero dake Kano.

Ya halarci manyan taruka na duniya a bangaren kiwon lafiya wadanda da yawa sun shafi lafiyar yara ne da na mata, cuta mai karya garkuwar jiki da kuma shugabanci a fannin lafiya.

Kamar yadda makusancinsa wanda Legit.ng ta samu jin ta bakinsa ya bayyana, Garba Yakasai mutumin kirki ne wanda ya mayar da hankali wurin ganin cigaba ta fannin lafiya.

Labari Da Duminsa: Farfesa Soyinka Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Kara karanta wannan

Harin cocin Ondo: Atiku ya bayar da gudunmawar miliyan N10 ga wadanda abun ya ritsa da su

A wani labari na daban, Farfesa Femi Soyinka, Farfesa masanin likitancin fata da garkuwar jiki, ya rasu. Kanin fitaccen marubucin nan ne na Afrika, Farfesa Wole Soyinka ne.

Kamar yadda takardar da iyalan Soyinka na Ake/Isara a jihar Ogun suka fitar, Farfesa Soyinka ya rasu a sa'o'in farko na ranar Talata, 14 ga Yunin 2022 a gidansa sa ke kauyen Kukumada na farin Ibadan, jihar Oyo.

Takardar ta samu sa hannun 'dan shi mai suna Ayodele a madadin iyalan, jaridar Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel