Gwamnan Kano ya nada sabbin kwamishinoni uku

Gwamnan Kano ya nada sabbin kwamishinoni uku

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya aika wa Majalisar Jihar sunayen kwamishinoni uku da ya zaba domin samun amincewar majalisar.

Kakakin Majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar a ranar Talata a Kano kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Gafasa ya ce gwamnan na neman amincewar majalisar domin nada Idris Garba a matsayin kwamishina kuma mamba na Majalisar Zartarwa na Jihar, SEC.

Ganduje ya nada sabbin kwamishinoni uku
Ganduje ya nada sabbin kwamishinoni uku. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An kama matar kwamandan Boko Haram (Hoto)

Ya ce gwamnan ya kuma nemi yan majalisar su tabbatar da nadin wasu kwamishinoni biyu a Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta na jihar, KANSIEC.

A cewarsa, ana sa ran Garba zai bayyana a gaban majalisar a ranar Laraba domin a tantance shi.

Ya bukaci wanda zai zo tantancewar kada ya taho da yan rakiya fiye da biyar don bin dokokin kare yaduwar COVID-19.

Mr Gafasa ya mika sunayen kwamishinonin na KANSIEC ga kwamitin majalisar ta Harkokin Zabe don gudanar da bincike a kansu tare da mika rahotonsu a ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a ranar Litinin ta ruwaito cewa gwamna Ganduje ya gabatar wa majalisar kasafin kudin shekarar 2020 da aka yi wa kwaskwarima domin samun amincewarsu.

Mr Ganduje ya ce an rage kasafin kudin ta kashi 30 cikin 100 domin tsaikon da aka samu a bangaren kudaden shiga sakamakon kallubalen da annobar coronavirus ta haifar a jihar da ma kasa baki daya.

Kudirin dokar na yi wa kasafin kudin garambawul ya wuce karantawa ta farko a majalisar kamar yadda NAN ta ruwaito.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo na jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje, ya ce jam'iyyar za ta yi duk yadda za ta iya don lashe zaben me gabatowa.

Ganduje ya ce Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike zai kasance a cibiyar killacewa ta jiharsa, kuma kafin ya warke za su ci zaben.

Ya ce kwamitin yakin neman zaben na cike da gogaggun 'yan siyasa da kuma matasa masu jini a jika.

Ya ce APC ta gano kokarin magudin zaben da PDP ke shirin yi kuma a shirye suke don bankade hakan.

Jam'iyyar PDP ta bayyana Gwamna Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zabenta na jihar Edo.

Amma yayin jawabi a ranar Litinin bayan kaddamar da kwamitin yakin neman zaben, Ganduje ya ce PDP tana goyon bayan Godwin Obaseki ne don suna son kwashe dukiyar da jihar ta tara don zaben.

Ganduje ya zargi Obaseki da butulci. Ya ce APC ce tsatsonsa amma duk da haka ya juya mata baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel