Kyawawan Hotuna da Bidiyon Kasaitaccen Shagalin Sunan 'Dan Hanan Buhari da Aka yi A Turai
- Shagalin kayataccen sunan jikan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zayd Muhammad Turad ya matukar kayatarwa
- An yi shagalin a bakin wani ruwa wanda aka kayatar da adon fulawoyi inda bakin alfarma suka halarta duk da ba a kasar nan aka yi ba
- Hanan Muhammadu Buhari tare da Muhammad Turad Sha'aban sun samu karuwar yaro namiji a watannin baya kuma sun shirya gagarumin taron suna
An yi kayataccen shagalin bikin sunan 'dan Hanan Buhari, Zayd Muhammad Turad bayan watanni da Muhammad Turad tare da Hanan Buhari suka samu karuwar yaro namiji.
Babu shakka shagalin bikin ya matukar kayatarwa duba da yadda ba a Najeriya aka yi shi ba.
A bidiyo da hotunan shagalin sunan wanda shafin @arewafamiliyweddings suka wallafa, an ga iyalan a Turai inda bakinsu suka dinga zuwa wurin shagalin sunan har da turawa.
Tsarin wurin taron sunan kadai ya isa ya fallasa maka irin manyan mutanen da suka halarta. An yi taron sunan ne gefen ruwa wanda aka kayatar ta hanyar yi masa kyale-kyale da fulawoyi masu matukar birgewa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jama'a da dama sun samu halarta wadanda suka hada da dangin Hanan Buhari irinsu Zahra Buhari, Halima Buhari da 'yar auta Nur Buhari.
Daga dangin ango kuwa, an ga mai gayya Hajiya Munira Buba Marwa, wacce ta fito cikin shigar alfarma kuma ta haske wurin sunan da salon adonta.
Asali: Legit.ng