Shehin Malamin Musulunci ya yi magana game da hadarin kin mallakar katin zabe

Shehin Malamin Musulunci ya yi magana game da hadarin kin mallakar katin zabe

  • Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi kira da babbar murya a kan mallakar katin zabe na PVC
  • Farfesan na jami’ar UDUS, Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya ce babu wani uzurin kin yin zabe
  • Bajimin Malamin yake cewa ko mutum ya kada kuri’a, ko bai yi ba, za a tsaida shugabanni a kasa

Sokoto - Babban malamin addinin Musulunci a Najeriya, Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto, ya yi kira ga mutane da su mallaki katin yin zabe.

Farfesa Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto ya yi amfani da shafinsa na Twitter a kwanakin baya, ya ankarar da jama'a kan muhimmancin zabe.

Shehin malamin hadisin ya ce akwai bukatar duk wanda bai da katin zabe na PVC, ya mallaka. A watan nan na Yuni za a rufe yin rajistar a Najeriya.

Kara karanta wannan

Na gazawa mutanena: Gwamnan Ondo ya fashe da kuka wiwi yayin binne wadanda harin coci ya ritsa da su

Kamar yadda malamin ya bayyana a shafin na sa, dole za a samu shugabannin da za su mulki al’umma ko mutum ya kada kuri’a, ko bai kada ba.

Saboda haka ya ce mutane ba su da dalilin kin neman katin PVC domin su kada kuri’arsu a 2023.

Mansur Sokoto wanda yake koyar da addini a jami’ar Usman Danfodio da ke garin Sokoto ya ce tsoron za a tafka magudin zabe ba uzuri ba ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar INEC
Shugaban INEC na kasa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

“Duk wanda bai da da katin zabe, ya yi gaggawar mallakar sa. Mu fahimci cewa ko mun yi zabe, ko ba mu yi ba, za a gudanar da zabe, kuma a zabi shugabannin da za su mulke mu.”
“A dalilin menene ba za mu zabi wadanda muke so a matsayin shugabanninmu ba.”
“Ba uzuri ba ne mutum ya fake da cewa za a murde zabe. Ubangiji ne ya ke bada mulki. Ya Allah, ka zaba mana shugaba na gari.”

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

- Mansur Sokoto

Daga baya babban malamin ya yi amfani da harshen Hausa, domin isar da sakon na sa ga al’umma.

“Duk wanda ba shi da katin zaɓe ya garzaya ya je ya yi. Ko mu yi zaɓe ko kar mu yi, sai an zaɓi shugabanni da za su jagorance mu. Me zai sa mu ba zamu zaɓi wadanda muke so su shugabance mu ba?”
“Ba uzuri ba ne mutum ya ce ai ko mun zaɓa, za a yi murɗiya. Allah shi ke ba da Mulki.”

- Mansur Sokoto

A zabi mutanen kirki

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Sheikh Salihu S. Abubakar ya yi irin wannan kira a hudubarsa ta ranar Juma’a a masallacin ITN da ke garin Zaria.

Salihu S. Abubakar ya ankarar da Musulmai a kan samun katin PVC domin zaben shugabanni. Malamin ya yi nasiha ne da a zabi na kwarai a kowane mataki.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan ta'adda sun harba bama-bamai a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Asali: Legit.ng

Online view pixel