44% na Mutanen Najeriya da suka je taimakawa Ukraine a yakin Rasha sun bakunci barzahu

44% na Mutanen Najeriya da suka je taimakawa Ukraine a yakin Rasha sun bakunci barzahu

  • Mutane 85 ne suka tashi daga Najeriya da zimmar taimakawa sojojin Ukraine a kan kasar Rasha
  • A karshe kusan 45% na wadannan sojoji haya sun mutu, wasu daga cikinsu kuma sun dawo Najeriya
  • Wata sanarwa ta bayyana cewa Dakarun Rasha sun hallaka sojojin haya kusan 2000 a Ukraine

Russia - Ana maganar mutane akalla 38 daga Najeriya da suke taimakawa kasar Ukraine a yakin da ta ke yi da Rasha, suka hallaka zuwa yanzu.

Wani rahoto da Rediyo Faransa ta fitar a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni 2022, ya tabbatar da cewa Najeriya ta yi asarar mutanenta 38 a Ukraine.

Ma’aikatar tsaro na kasar Rasha ta fitar da alkaluma a game da yakin da ake yi da Ukraine, ta ce an samu sojojin hayan Najeriya da aka kashe.

Kara karanta wannan

Yadda fasinjoji 18 suka kone kurmus a wani hatsari da afku a jihar Neja

Akwai mutane kusan 85 daga Najeriya da suka yi karfin hali, su ka shiga Ukraine da nufin ba kasar agaji a kan sojojin Vladimir Putin na Rasha.

Wasu sojojin haya sun arce

Daga cikin wadannan sojojin haya, an kashe 38, sannan kuma 35 sun koma inda suka fito. RFI ta ce mutum 12 aka bari yanzu suna cigaba da yaki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda gwamnatin Rasha ta sanar, ta ce makudan kudin da Ukraine ke biyan sojojin hayan, wannan bai hana dakarun Rasha aika su barzahu ba.

Sojan Rasha
Daya daga cikin Sojojin Rasha Hoto: emerging-europe.com
Asali: UGC

Adadin mutanen da suka shiga Ukraine domin taimakawa kasar sun haura 1000 inji kasar Rashar.

Daga makwabta Poland kawai, akwai sojojin haya 1831 da ke taimakawa Ukraine. A cikinsu ana tunanin kimanin 370 sun mutu a wajen gumurzun.

Sojojin haya 272 da suke taimakon Ukraine a wannan yaki sun gaji, duk sun koma kasashensu.

Kara karanta wannan

Harin Kwantar Bauna: Yan Ta'adda Sun Kashe Manjo Na Soja, Sun Kona Motar Sojoji Sun Sace Makamai a Niger

Ma’aikatar tsaro ta kasar Rasha ta ce zuwa yanzu akwai sojoji 3321 na haya da suke cigaba da yakarta, har yanzu ba a iya ganin bayan wadannan ba.

Gaba daya dai Rasha ta kashe sojojin haya 1956, a ciki ne aka samu 38 daga Najeriya. Mutane 1700 da suka je ba Ukraine agaji, sun tsere zuwa gida yanzu.

Ukraine ta yi asara

Tun a baya aka ji cewa sojoji 1, 300 kasar Ukraine ta rasa tun daga lokacin da Rasha ta shigo mata da yaki zuwa tsakiyar watan Maris na shekarar nan.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce kafin sojan Ukraine daya ya mutu, sai an kashewa Rasha sojojinta akalla 10 a yakin da aka yi a kasarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel