Adadin yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya ya kai milyan 18, Gidauniyar McArthur

Adadin yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya ya kai milyan 18, Gidauniyar McArthur

  • Bincike ya nuna cewa adadin yara maras zuwa makaranta a Najeriya ya tashi daga milyan 10 zuwa 18, gidauniyar MacAuthur
  • Wannan ya biyo bayan kalaman bankin duniya da majalisar dinkin duniya da lalacewar ilimi a Najeriya
  • Asusun lamunin UNICEF ya bayyana cewa bincike ya nuna mafi akasarin yara a makarantun firamare kawai zuwa suke yi

Abuja - Gidauniyar MacArthur ta bayyana cewa duk da kudi N100trn da gwamnatin Najeriya tayi ikirarin kashewa kan Ilimi daga 1999 zuwa yanzu, adadin yaran da basu zuwa makaranta ya kusa milyan ashirin.

Gidauniyar tace adadin yara ya tashi daga 10.5 milyan zuwa 18 milyan.

Mataimakin Diraktan gidauniyar dake Najeriya, Dayo Olajide, ya bayyana haka a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja wajen taron tattaunawa kan ayyukan mazabu da yakin neman zaben 2023.

OrderPaper, BudgIT da gidauniyar MacAuthur ne suka shirya zaman, rahoton DailyTrust.

Yace:

"Ina kudi sama da N100 trillion da aka kashe? Yan Najeriya na tashi kulli yaumin suna tambayar juna shin menene amfanin kasafin kudi garesu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban kungiyar BudgIT kuwa, Gabriel Okiewu, ya ce duk da makudan kudaden yan majalisu 469 ke samu, gwamnoni, yan majalisar jiha, ciyamomin kananan hukuma da kansiloli, har yanzu an gaza biyan bukatar al'umma.

Yarah
Adadin yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya ya kai milyan 18, Gidauniyar McArthur

Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF

Kwanakin baya, Asusun lamunin yara na majalisar dinkin duniya watau UNICEF ya ce kashi 70 cikin 100 na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai da ake koya musu a makaranta.

Masanin sadarwa na UNICEF, Mr Geoffrey Njoku, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a jihar Kano lokacin taron tattaunawa da manema labarai kan Sustainable Development Goals (SDGs).

A cewarsa, babban amfanin zuwa makaranta shine yaro ya iya karatu da lissafi na fari, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.

Hakazalika, Mr Rahama Farah, shugaban ofishin UNICEF dake Kano ya ce UNICEF da gwamnatin jihar Kano na hada kai wajen inganta ilmin Boko amma da sauran rina a kaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel