Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF

Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF

  • Asusun lamunin UNICEF ya bayyana cewa bincike ya nuna mafi akasarin yara a makarantun firamare kawai zuwa suke yi
  • Bankin Duniya kuwa ya ce a nasa binciken kashi 70% na daliban makarantu ko jumla daya basu iya rubutawa
  • Sun yi kira ga horar da Malaman makarantun da kuma sauya manhajar karatu

Kano - Asusun lamunin yara na majalisar dinkin duniya watau UNICEF ya ce kashi 70 cikin 100 na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai da ake koya musu a makaranta.

Masanin sadarwa na UNICEF, Mr Geoffrey Njoku, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a jihar Kano lokacin taron tattaunawa da manema labarai kan Sustainable Development Goals (SDGs).

A cewarsa, babban amfanin zuwa makaranta shine yaro ya iya karatu da lissafi na fari, rahoton kamfanin dillancin labarai NAN.

Kara karanta wannan

Masu fasa bututu sun taso Najeriya a gaba, ana asarar Naira Biliyan 600 a kowace rana

Yace:

"Tun 2010, mun yi kokarin magance matsalar yara milyan 10.5 da basu zuwa makaranta, amma duk da haka kashi 70% na yaran dake makarantar basu fahimtar darasi."
"Ya kamata mu hada adadin kashi 70% din nan kan milyan 10.5 da basu zuwa makaranta gaba daya don a maida hankali sosai kan lamarin."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wajibi mu kawo sauyi bangaren ilimi ta hanyar horar da Malamai, canza manhajin karatu."

Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF
Kashi 70% na yan makarantun firamare a Najeriya basu fahimtar komai, UNICEF
Asali: Getty Images

Yan shekaru 10 basu fahimtar jumla daya a Turanci

Hakazalika, Mr Rahama Farah, shugaban ofishin UNICEF dake Kano ya ce UNICEF da gwamnatin jihar Kano na hada kai wajen inganta ilmin Boko amma d sauran rina a kaba.

Farah, wanda ya samu wakilcin Elhadji Diop, ya ce:

"A cewar bankin duniya, Najeriya na fama da talaucin Ilimi saboda kashi 70% na yara yan shekara 10 basu iya hada jumla daya ko dan lissafi mai sauki."

Kara karanta wannan

Musulmai sun caccaki gwamnan Ondo kan shirin dankawa Kiristoci wasu makarantu

"Saboda wajibi ne mu janyo hankalin masu ruwa da tsaki don magance matsalolin talauci a kasa.

Bugu da kari, Dr Chidi Ezinwa, Malami a tsangayar karatun jarida a jami'ar kimiya da fasaha dake Enugu yace cimma SDG's ba zai yiwu muddin ba'a cikka hakkin yara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel