Bayan shekaru 8: Sojoji sun ceto Hauwa Joseph, yar matar Chibok da Boko Haram suka sace tare da diyarta
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun ceto wata yar makarantar Chibok, Hauwa Joseph da diyarta
- Hauwa na daya daga cikin yan makarantar Chibok 276 da Boko Haram suka sace a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
- Rundunar sojin ta bayyana cewa a yanzu haka yar Chibok din da diyarta suna a cibiyar kiwon lafiya ta sojoji
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Borno - Rundunar yan sandan Najeriya ta ceto Hauwa Joseph, daya daga cikin ‘yan matan da Boko Haram suka yi garkuwa da su a makarantar Sakandaren ’yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok.
A wata wallafa da shafin rundunar ta yi a Twitter, ta bayyana cewa dakarunta ne suka gano Hauwa a ranar 14 ga watan Yunin 2022 tare da yarta a yayin da suke wani aikin sintiri.
Yan ta’addan Boko Haram ne suka sace yan matan na makarantar Chibok su 276 a ranar 14 ga watan Afrilun 2014, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Kamar yadda rundunar ta bayyana, Hauwa da diyar tata suna nan a cibiyar kiwon lafiya ta sojoji.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sakon da rundunar ta wallafa na cewa:
“Dakarun sojoji a yayin aikin kakkaba a ranar 14 ga watan Yunin 2022 sun sake kama wata yarinya da aka sace daga makarantar GGSS Chibok mai suna Hauwa Joseph, wacce yan Boko Haram suka yi garkuwa da ita a ranar 14 ga watan Afrilu 2014.
“Yar makarantar Chibok din da aka gano da diyarta na a cibiyar kiwon lafiya ta sojoji a yanzu haka.”
Boko Haram sun sheke na kusa da Shekau bayan yunkurin mika kansa ga sojoji
A wani labarin, ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP sun kawar da daya daga cikin manyan kwamandojin su Abu-Sadiq wanda aka fi sani da Burbur bisa zarginsa da shirin mika wuya ga dakarun gwamnati.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa an kashe Burbur ne a kauyen Galta da ke kusa da Madagali bayan tuhumarsa da laifin cin amana a wata kotun 'yan ta'adda ta Ya-Shaik, ISWAP Fiye na dajin Sambisa.
A cewar wani rahoton sirri da aka samu daga majiyar soji ta bayyana cewa, Bubur ya kasance a gidan yari na ISWAP a watan Afrilu bayan da aka kama shi hannu dumu-dumu yana shirin mika kansa ga soji. A karshe an kashe shi a ranar 9 ga Mayu, 2022.
Asali: Legit.ng