Zamfara: Akwai Yiwuwar Gwamnati Za Ta Sake Rufe Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Karo Na 2

Zamfara: Akwai Yiwuwar Gwamnati Za Ta Sake Rufe Hanyoyin Sadarwa Na Zamani Karo Na 2

  • Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta iya sake rufe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar idan bukatar hakan ta sake tasowa
  • Zailani Bappa, hadimin Gwamna Bello Matawalle ne ya yi wannan karin bayanin yana mai cewa amma a yanzu gwamnan bai bada umurin a rufe hanyoyin sadarwan ba
  • Gwamnatin na Jihar Zamfara ta jajantawa iyalan mutanen da yan bindiga suka sace a baya-bayan nan a Bebeji Plaza ta kuma ce tana aiki da hukumomin tsaro da aiwatar da wasu sabbin tsare-tsare

Jihar Zamfara - Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana cewa akwai yiwuwar ta sake katse hanyoyin sadarwa na zamani a jihar karo na biyu idan bukatar hakan ya taso.

Mashawarcin Gwamna Matawalle na musamman kan kafafen watsa labarai, Zailani Bappa, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce gwamnatin ba ta riga ta datse hanyoyin sadarwar ba kamar yadda ake yadda jita-jita, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan APC ya sha bam-bam, bai goyon-bayan Bola Tinubu ya dauki Musulmi

Gwamna Bello Matawalle.
KallubalenTsaro: Akwai Yiwuwar Gwamnatin Zamfara Ta Sake Rufe Hanyoyin Sadarwa. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma, ya ce, 'Idan bukatar datse hanyoyin sadarwar ya taso, ana iya sake datse hanyoyin sadarwar.'

Bappa ya jadada cewa ya zama dole ya yi karin haske kan wasu labarai marasa tushe da aka ce sun fito daga ofishinsa game da rufe hanyoyin sadarwar a jihar.

Kalamansa"

"Mai Girma, Dr Bello Mohammed Matawalle, ya nuna damuwarsa bisa hare-haren yan bindiga a jihar, da kulawa da wadanda abin ya shafa ya kuma jajantawa iyalan wadanda aka sace a Bebeji Plaza a baya-bayan nan.
"Ba jajantawa kawai gwamnati za ta yi ba kaman kowa, amma ta sanar da al'umma matakan da ta dauka don magance kallubalen.
"Don haka, Mai Girma gwamna ya bayyana matsayin gwamnati a wannan lokacin.
"Mai girma ya ce ya tuntubi dukkan hukumomin tsaro a jihar don bullo da sabon tsari don magance kallubalen da yan bindigan, musamman yanzu da damina ya zo, wanda zai bada daman a aiwatar da sabbin matakan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

"Ya kuma ce idan bukatar rufe hanyoyin sadarwa ta taso, za a sake iya yin hakan.
"Amma mai girma gwamna bai sanar da rufe hanyoyin sadarwa ba, kuma bai umurci hukumomin su aiwatar haka ba.
"Wannan shine gaskiyar abin da ya faru."

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel