Kotu zata yanke hukunci kan makashin Hanifa Abubakar ranar 28 ga watan Yuli

Kotu zata yanke hukunci kan makashin Hanifa Abubakar ranar 28 ga watan Yuli

  • Bayan shafe watanni ana zaman sauraron shaidu, Babbar Kotun Kano zata yanke hukunci kan mutanen da ake zargi da kisan Hanifa
  • Alƙalin babbar Kotun jihar Kano, Mai shari'a Usman Na'abba, ya saka ranar 28 ga watan Yuli, 2022 don sanin makomar Abdulmalik Tanko da sauran mutum 2
  • A zaman yau Talata, lauyan masu gabatar da ƙara ya roki Kotu ta duba hujjojin da ke gabanta ta yanke wa mutanen hukuncin kisa

Kano - Babbar Kotun Kano da ke zamanta a Audu Baƙo, ta sanya ranar 28 ga watan Yuli, 2022 domin yanke hukunci kan shari'ar kisan Hanifa Abubakar, yar shekara biyar.

Ana zargin shugaban makarantar da Hanifa ke karatu, Abdulmalik Tanko, da garkuwa haɗe da kisan yarinyar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yankewa 2 daga abokan harkallar Abba Kyari hukunci

Alƙalin Kotun, Mai shari'a Usman Na'abba, ya zaɓi ranar ne a zaman ranar Talata bayan zartar da jawabin rubutu na ƙarshe da kowane ɓangarori suka yi.

Babban wanda ake zargi, Abdulmalik Tanko.
Kotu ta zata yanke hukunci kan makashin Hanifa Abubakar ranar 28 ga watan Yuli Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnatin Kano ta gurfanar da mutum uku; Abdulmalik Tanko, tare da waɗan da suka haɗa kai, Hashin Isiyaku, da Fatima Jibril Musa, gaban Kotun bisa tuhume-tuhume guda biyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuhume-tuhumen sun haɗa da haɗa kai wajen aikata babban laifi, garkuwa, ɗaurin wuri ɗaya da kuma mummunan kisan kai wanda ya saba wa sashin 97, 274, 277, 221 na kundin fanel kod.

Yadda zaman yau Talata ya gudana

A zaman na yau Talata, lauya mai gabatar da ƙara, Lamido Abba Soron Dinki, ya roƙi Kotun ta duba hujjojin da aka baje mata ta tabbatar da laifin waɗan da ake ƙara kuma ta yanke musu hukuncin kisa.

A jawabinsa ya ce:

Kara karanta wannan

Aikin Allah: Bidiyon yadda wani mutumi ya shiga ya tuƙa Tankar Fetur mai ci da wuta don ya ceci mutane

"Muna rokon Kotu ta yanke musu hukuncin kisa su duka saboda hukuncin waɗan nan sashin da ake tuhumar su da saɓa wa ya kunshi hukunci ɗaya ne kisa."

Legit.ng Hausa ta tattaro muku cewa a ranar 4 ga watan Disamba, 2021 aka sace Hanifa yayin da take kan hanyar komawa gida daga Islamiyya kuma daga baya aka gano cewa an kashe ta.

Da farko, Tanko ya amince ya yi amfani da maganin Ɓera na N100 wajen kasheta da ɓinne ta a ɗaya daga cikin makarantunsa, amma daga baya ya canza magana da cewa sace ta kaɗai ya yi.

A wani labarin na daban kuma Sabbin bayani masu ƙarfi sun bayyana wanda PDP zata tsayar mataimakin ɗan takararta wato Atiku Abubakar

Har yanzun jam'iyyun siyasa a Najeriya sun gaza samun matsaya kan waɗan da zasu kasance mataimakan yan takararsu na shugaban kasa.

A ɓangaren babbar jam'iyyar hamayya PDP, alamu masu karfi sun nuna cewa gwamna Okowa na jihar Delta ke kan gaba.

Kara karanta wannan

Kano: Gwanayen Alƙur'ani da dubbanin mutane sun gudanar da Addu'o'i ta musamman kan zaɓen 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel