Kwastoma da abokansa sun kashe Karuwa Musulma don sun ga Al-Qur'ani cikin dakinta

Kwastoma da abokansa sun kashe Karuwa Musulma don sun ga Al-Qur'ani cikin dakinta

  • An gurfanar da wasu matasa uku gaban kotu dake jihar Legas kan laifin kashe wata yarinya tare da banka mata wuta
  • Matasan sun tuhumi yarinyar da laifin ajiye Al-Qur'ani cikin daki duk da kasancewarta yar gidar magajiya
  • Daya daga cikn matasan ya shiga wajenta biyan bukatarsa kuma ya sace mata kudi N5000

Hukumar yan sandan jihar Legas ta damke wasu matasa uku kan laifin kashe wata karuwa mai suna , Hannatu Salihu, da banka mata wuta don sun ga Al-Qur'ani cikin dakinta.

Punch ta ruwaito cewa daya daga cikin matasan ya shiga dakin Hannatu yin lalata da ita kuma ya biyata kudi N1000.

Daga bisani ta lura ya kwamushe mata kudi N5000 da ta ajiye cikin dakin.

Sai ta tuhumesa da yi mata sata har abin ya kaure ya zama fada.

Kara karanta wannan

Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

Sai matashin ya kira abokansa cewa a duba dakin Hannatu don tabbatar da gaskiyar batan kudin N5000.

Kwatsam sai suka ga Al-Qur'ani karkashin matashin kai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yan sanda
Kwastoma da abokansa sun kashe Karuwa Musulma don sun ga Al-Qur'ani cikin dakinta
Asali: Facebook

Wata majiya ta bayyana cewa sai suka tambayeta shin me ya hada karuwa da Al-Qur'ani? kawai sai suka far mata, suka lallasata har lahira kuma suka kona gawarta.

A cewar majiyar:

"Abinda ya faru shine yarinyar karuwa ce kuma wani kwastomanta ya kai ziyara kuma ya biya N1000 bayan biyan bukatarsa."
"Amma yayinda ya fita daga dakin, sai ta gano ya dauke mata N5000. Matasan dake tare da mutumin suka tambayeta shin ta tabbatar shi ya dauka? Sai suka ce bari su shiga dakinta don tabbatar da hakan."
"Yayinda suke bincikar dakin, sau suka tsinci Al-Qur'ani karkashin Pillow kuma suka fara tuhumarta shin me take da Al-Qur'ani. Sai suka fara dukanta, suka caka mata wuka kuma suka kona ta."

Kara karanta wannan

Magidanci na tsaka da ciwo, matarsa tayi wuff da makwabcinsa da suke katanga daya

"Wannan abu ya faru a Alaba Rago. Ita ma yarinyar yar Arewa ce."

Kakakin hukumar yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin ya tabbatar da rahoton.

An gurfanar da matasan gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel