Magidanci na tsaka da ciwo, matarsa tayi wuff da makwabcinsa da suke katanga daya

Magidanci na tsaka da ciwo, matarsa tayi wuff da makwabcinsa da suke katanga daya

  • Wani dattijo dan kasar Zambia na jinyar ciwon da ya yi sanadiyyar shanyewar barin jikinsa a 2021 da kuma yaudararsa da matarsa tayi
  • Mutumin mai suna Rabison Mawere ya bayyana yadda matarsa tayi watsi dashi gami da auren makwabcinsu na kusa bayan ciwon ya kwantar da shi kakas
  • Dattijon mai shekaru 51, wanda a halin yanzu bai da mai kula dashi ko agaza masa ya yi kira da mutane da su kawo masa dauki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mazauna wani kauye a kasar Zambia sun cika da mamaki bayan wata mata tayi wuff da makwabcin da katangarsu ke jikin gidansa bayan mijinta ya kwanta jinya tsawon shekaru tare da samun matsalar shanyewar barin yiki.

A watan Oktoba 2021, mutumin mai suna Rabison Mawere ya labarta yadda wata matsalar rashin lafiyar da ta hanasa gudanar da rayuwarsa yadda ya dace ya kama shi.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan bindiga sun sheke rayuka 17, sun sace 'yan China 4 a wurin hakar ma'adanai

Rabison Mawere
Magidanci na tsaka da ciwo, matarsa tayi wuff da makwabcinsa da suke katanga daya. Hoto daga ABN TV
Asali: UGC

Yayi mamakin abinda matarsa tayi

Yayin zantawa da Zambia ABN TV, Mawere ya ce ya matukar shan mamaki gami da shiga cikin wani yanayin damuwa bayan ciwonsa ya ta'azzara sannan masoyiyarsa ta tsawon zamani tayi watsi dashi ba tare da tausayi ba gami da aure makwabcin da suke katanga daya dashi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, rayuwa ta yi masa kunci tun lokacin da ya kwanta ciwon, sannan akwai lokacin da yake kwanciya ba tare da sanya komai ba a bakinsa ba.

Haka zalika, mutumin mai shekaru 51 ya koka kan yadda aka sallamesa daga asibiti duk da bai da lafiya.

A cewar abokin Mawere Williams, abokinsa ya dauki tsawon lokacin yana shan matukar wahala, sannan watsi dashi da matarsa tayi ya kara masa gishiri a ciwonsa.

Dattijon na kira ga mutanen al'umma masu hannu da shuni da na kwarai da su taimaka masa wajen neman lafiyarsa, kayan abinci da makwanci mai kyau.

Kara karanta wannan

Yadda aka Halaka Wani Mutum Saboda ya Goyi Bayan Batanci ga Annabi

Hotuna da Bidiyon Kyakyawar Budurwa da Tace Zata Baiwa Ɗiyar Ekweremadu Kyautar Ƙoda

A wani labari na daban, wwata matashiya 'yar Illorin mai suna Martha Uche ta bayyana yadda ta shirya sadaukar da kodarta don ceto rayuwar 'diyar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekwdremadu.

Idan za a tuna, 'yan sanda birnin London suna zargin Ekweremadu da matarsa Beatrice da laifin safarar wani yaro zuwa Amurka don cire sassan jikinsa, kamar yadda hukumar shari'ar ta bayyana a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni.

Miss Martha Uche ta ce a shirye ta ke da ta sadaukar da kodarta don ceto rayuwar 'diyar Ike Ekwdremadu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel