EFCC Ta Sako Hadimin Zulum Da Ta Kama Kan Wallafa a Facebook Game Da Damfarar Akanta Janar

EFCC Ta Sako Hadimin Zulum Da Ta Kama Kan Wallafa a Facebook Game Da Damfarar Akanta Janar

  • Hukumar yaki da almundahana tare hana yiwa tattalin arzirkin kasa zagon kasa ta sako babban hadimin gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, wanda ta cafke
  • Kamen yazo ne bayan wata wallafa da ya yi inda ya ce ana jita-jitar wani fitaccen 'dan majalisa daga Borno na da alaka da damfarar N80 biliyan da akanta janar na tarayya ya sace
  • Majiya ta ce, gwamna Zulum ya kira shugaban EFCC na yankin tare da jin ba'asin da yasa suka rike babban hadimin nasa, inda suka yi alkawarin sakinsa a safiyar Juma'a

Borno - Hukumar yaki da cin hanci tare da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa ta saki Abdullahi Yusuf, babban hadimin Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno.

Kara karanta wannan

Dan Dora Akunyili: Fastoci Sun Rika Tatsar Kudin Mahaifiyana Da Sunan Za Su Yi Mata Maganin Cutar Kansa

Yusuf ya yi wallafa a ranar 29 ga watan Mayu, inda yake cewa ana jita-jitar wani fitaccen 'dan majalisa daga Borno na da alaka da damfar N80 biliyan da ke da alaka da Ahmed Idris, akanta janar na tarayya.

EFCC Ta Sako Hadimin Zulum Da Ta Kama Kan Wallafa a Facebook Game Da Damfarar Akanta Janar
EFCC Ta Sako Hadimin Zulum Da Ta Kama Kan Wallafa a Facebook Game Da Damfarar Akanta Janar. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Duk da dai hadimin bai ambaci suna ba, magoya bayan 'dan majalisar da ke wakiltar mazabar Biu sun je karkashin wallafar tare da zargin da 'dan majalisar ya ke, The Cable ta ruwaito.

Saboda haka ne EFCC suka gayyaci Yusuf ofishinsu na Maiduguri.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ruwaito yadda ya isa ofishin EFCC washe garin ranar daga bisani suka tsare shi, duk da irin yadda iyalinsa suka yi kokarin ganin an sako shi amma abun ya gagara.

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, an sako Yusuf a ranar Juma'a bayan Zulum ya sa baki.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 74, an sako mutum 11 cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Gwamnan ya kira shugaban ofishin EFCC na yankin, tare da neman sanin ba'asin da yasa aka rike hadimin.

"Ubangidanmu ya bayyana mana yadda gwamna ya kira sa a kan kama Yusuf da aka yi. Ran gwamnan ya matukar baci," a cewar majiyar.
"A takaice dai, ubangidanmu ya ce gwamnan ya so zuwa ofishin don ya hadu da Yusuf, kafin shugaban yankin ya bashi tabbacin za a sake shi a safiyar Juma'a."

Haka zalika, EFCC ta maka Yusuf babban kotun tarayya bisa karya dokar tattalin arzirkin ta 2004. Sai dai, hadimin bai gurfana ba kafin a sako shi ranar Juma'a.

EFCC ta Ayyana Neman Fitaccen Fasto da Matarsa Kan Damfarar N2bn

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa na neman wasu ma'aurata, Onyimmiebi (Miebi Baraza) da Beatrice Bribena ruwa a jallo.

A wata takarda da kakakin hukumar, Wilson Uwujaren ya rattaba hannu, EFCC tana neman ma'auratan ne ruwa a jallo bisa zarginsu da damfarar 'yan Najeriya N2 biliyan, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An jikkata wasu da dama yayin da rikici ya barke tsakanin Hausawa da Inyamurai yan kasuwa a Edo

Asali: Legit.ng

Online view pixel