Guje wa Kamen EFCC: 'Yar Kasuwa ta Sheka Lahira Bayan ta Garkame Kanta a Bandaki

Guje wa Kamen EFCC: 'Yar Kasuwa ta Sheka Lahira Bayan ta Garkame Kanta a Bandaki

  • Wata 'yar kasuwa da ke zaune a birnin Legas ta garkame kanta a bandaki gami da rasa ranta yayin da jami'an EFCC suka dira gidanta don kama ta
  • Kakakin 'yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami'an hukumar sun yi kokarin kama marigayiyar saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba
  • Olufunmbi Jaiyeola ta ki ba su damar shiga gidan na tsawon awanni, daga bisani wani 'dan uwanta ya musu isoinda aka tsince ta a bandaki bakinta na kumfa

Legas - Wata 'yar kasuwa da ke zaune a Legas ta rasa ranta bayan ta garkame kanta a bandaki yayin da jami'an Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arzirkin kasa zagon kasa (EFCC) suka yi yunkurin kama ta.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

Benjamin Hundeyin, kakakin 'yan sandan Legas, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga The Cable Lifestyle a ranar Lahadi.

Guje wa Kamen EFCC: 'Yar Kasuwa ta Sheka Lahira Bayan ta Garkame Kanta a Bandaki
Guje wa Kamen EFCC: 'Yar Kasuwa ta Sheka Lahira Bayan ta Garkame Kanta a Bandaki. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ya ce lamarin ya auku ne ranar 2 ga watan Yuni a gida mai lamba 15 layin Dele Onabule na Magodo Brooks cikin Legas.

Hundeyin ya bayyana yadda jami'an EFCC suka dira gidan marigayiyar don su kama ta a kan dalilan da ba a bayyana ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, matar mai suna Olufunmbi Jaiyeola ta ki yi wa jami'an iso zuwa cikin gidan na tsawon awanni.

Kakakin ya bayyana yadda daga bisani jami'an suka samu damar shiga gidan tare da taimakon wani 'dan uwanta.

Sai dai, an gano yadda Jaiyeola ta garkame kanta a bandakinta. Hundeyin ya ce EFCC sun shiga don su kama ta, amma suka ga bakin matar na kumfa.

"EFCC kun kawo mana rahoto a ofishinmu misalin karfe 8:30 na dare. Jami'an sun zo ne daga ofishin EFCC na Ikoyi," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Babban Faston Cocin Ondo ya Labarta Yadda Harin Ya Kasance

"Matar ta ki fitowa. Ta garkame kanta a bandaki wanda hakan ya dauki tsawon awanni. Yayin da wasu 'yan uwanta suka ba su damar shiga bandakin sun tarar da bakin ta na kumfa.
"An yi zargi guba ta sha. An garzaya da ita asibitin Lagoon a Adeniyi Jones cikin Ikeja inda rai ya yi halin shi. 'Yan sandan sun ziyarci wurin don bincikar hakikanin abun da ya faru.
"Sai dai fusatatun 'yan uwanta sun ki ba wa 'yan sanda damar shiga gidan. EFCC sun fitar da takarda game da aukuwar lamarin sannan ana cigaba da bincike," yace.

EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

A wani labari na daban, Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi watattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da dan takarar shugabancin kasa na APC daga jihar Imo, Rochas Okorocha, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

Okorocha, wanda a halin yanzu ya ke wakiltar mazabar Imo ta yamma a majalisar dattawa, an gurfanar da shi gaban mai shari'a Inyang Ekwo a ranar Litinin, Channels Tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel