Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya yi martani a kan harin da tsagerun yan bindiga suka kai cocin katolika na St Francis a karamar hukumar Owo
  • Akeredolu ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki tare da shan alwashin kamo maharan da hukunta su
  • Harin wanda aka kaddamar a yau Lahadi, 5 ga watan Yuni, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce gwamnatinsa za ta kamo wadanda suka kai hari kan wani coci a karamar hukumar Owo ta jihar, jaridar The Cable ta rahoto.

A yau Lahadi, 5 ga watan Yuni ne wasu yan bindiga suka farmaki cocin katolika na St Francis yayin da ake shirin tashi.

An tattaro cewa mutane da dama sun mutu a harin ciki harda yara da mata.

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani
Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

An kuma rahoto cewa yan bindigar sun tayar da bam kafin suka bude wuta a kan masu bautan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin mugunta da shaidanci, ya kuma ce hakan cin zarafi ne ga mutanen Owo.

Ya ce:

“Bakar Lahadi ce a Owo. Zukatanmu sun yi nauyi. Makiyan mutane sun farmaki zaman lafiyanmu. Wannan rashi ne na kashin kai, hari kan jaharmu mai albarka.
“Na yi magana da limamin darikar Katolika na Ondo, Most Reverend Jude Arogundade, wanda a yanzu haka yake kan hanyarsa ta zuwa Owo. Hakazalika, dole na yanke aikin jam’iyyata ta kasa a Abuja sannan na ziyarci Owo cikin gaggawa.
“Wannan wani lamari ne da ba a zata ba. Na shiga dimuwa a takaice. Duk da haka, za mu bi duk wata hanya don farautar wadannan mahara sannan mu sa su biyan bashi. Ba za mu taba saduda ga makirce-makircen marasa imani ba a kudurinmu na kawar da jihar mu daga masu aikata laifuka."

Da dumi-dumi: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo

A baya mun ji cewa wasu da ake zaton yan ta’adda ne sun tayar da cocin Katolika na St Francis a Owo, hedkwatar karamar hukumar Owo ta jihar Ondo.

Rahotanni da ke fitowa sun bayyana cewa masu bauta da dama sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata bayan tashin bam a cocin wanda ke kusa da fadar Olowo na Owo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel