Tashin Hankali: Babban Faston Cocin Ondo ya Labarta Yadda Harin Ya Kasance

Tashin Hankali: Babban Faston Cocin Ondo ya Labarta Yadda Harin Ya Kasance

  • Rabaran Andrew Abayomi, daya daga cikin fastocin majami'ar Katolika ta St Francis da 'yan ta'adda suka tada bom ya labarta yadda harin ya auku
  • An gano yadda masu bauta da dama suka rasa rayukansu yayin da hatsabiban suka tada bom a majami'ar a safiyar Lahadi ana gab da kammala bautar ranar
  • Gwamna Rotimi Akeredolu ya yi jaje ga wadanda lamarin ya auku da su tare da daukar alwashin zakulo wadanda ke da alhaki a kai farmakin kasancewar garin a mahaifarsa

Ondo - Rabaran Andrew Abayomi, daya daga cikin fastocin majami'ar Katolika ta St Francis ta titin Owa-luwa a Owo da ke jihar Ondo, ya labarta yadda aka kai wa majami'ar farmaki.

Daily Trust ta ruwaito yadda masu bauta da dama suka rasa rayukansu yayin da 'yan ta'adda suka tada bom a majami'ar a safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

Tashin Hankali: Babban Faston Cocin Ondo ya Labarta Yadda Harin Ya Kasance
Tashin Hankali: Babban Faston Cocin Ondo ya Labarta Yadda Harin Ya Kasance. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wata tattaunawa da BBC harshen Yarbanci, faston ya ce wadanda ake zargin 'yan ta'addan sun shiga ne yayin da ake dab da kammala bautar ranar.

"Muna kokarin kammala ibadar ranar. Har na fara ce wa mutane su fara tafiya, a nan ne muka fara jin karar bindiga ta ko ina."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun boye cikin majami'ar amma wasu sun riga sun tafi yayin da aka kai harin. Mun garkame kawunanmu a majami'ar na tsawon mintoci 20. A lokacin da mu ji sun tafi, muka bude majami'ar tare da garzayawa da wadanda lamarin ya auku da su asibiti."

Gwamna Rotimi Akeredolu ya yi martani game da lamarin, wanda ya auku a mahaifarsa.

Ya siffanta harin a matsayin "rashin imani da shaidanci", inda yake cewa hakan tada hankula ne ga mutanen Owo da ke kaunar zaman lafiya a masarautar Owo wadanda suka dandani gardin zaman lafiya na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Mai saida askirim, dillalin tumatir: Shettima ya nemi gafarar Osinbajo da Lawan kan cin zarafinsu da yayi

"Wata bakar Lahadi ce a Owo. Zuciyoyinmu sun yi nauyi. Makiyanmu sun kai farmaki ga zaman lafiya da kwanciyar hankalinmu. Wannan rashi ne da ya shafe mu, hari ga jihar mu. Na yi magana da Bishop na yankin katolikan Ondo, mai girma Rabaran Jude Arogundade, wanda a halin yanzu yake kan hanyarsa ta zuwa Owo.
"Hakazalika, dole tasa na bar hidimar jam'iyya t a Abuja don in ziyarci Owo cikin gaggawa."
"Lamarin ya auku babu za to ba tsammani. Tashin hankali ya hana ni faruci mai yawa.
"Ba tare da kasa a guiwa ba, za mu yi iya kokarin ganin mun faruci wadannan maharan don su dandana kudarsu. Ba za mu taba mika wuya ga azzaluman da ke son tarwatsa mana jiha ba.
"Ina yi wa mutane na na Owo jaje, musamman iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan farmakin. Ina mika ta'aziyyata ga Olowo na Owo, Oba Gbadegesin Ogunoye tare da majami'ar Katolika.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Mutane da dama sun mutu yayin da bam ya tashi a cocin Katolika da ke Ondo

"Ina rokon jama'armu da su natsu sannan su sa ido. Kada ku dauki doka a hannayenku. Na yi magana da shugabannin hukumomin tsaro. Sannan sun bani tabbacin za a turo da jami'an tsaron da za su dinga lura da dawo da kwanciyar hankalin masarautar Owo." A cewar Akeredolu.

Harin coci a Ondo: Za mu zakulo miyagun kuma sai sun biya bashi, Gwamna Akeredolu ya yi martani

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya ce gwamnatinsa za ta kamo wadanda suka kai hari kan wani coci a karamar hukumar Owo ta jihar, jaridar The Cable ta rahoto.

A yau Lahadi, 5 ga watan Yuni ne wasu yan bindiga suka farmaki cocin katolika na St Francis yayin da ake shirin tashi. An tattaro cewa mutane da dama sun mutu a harin ciki harda yara da mata.

An kuma rahoto cewa yan bindigar sun tayar da bam kafin suka bude wuta a kan masu bautan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel