Kano: Mutum 201 na Kwance Rai a Hannun Allah a Asibiti Bayan Shakar Kemikal a Sharada

Kano: Mutum 201 na Kwance Rai a Hannun Allah a Asibiti Bayan Shakar Kemikal a Sharada

  • Mutum 201 aka kwasa rai a hannun Allah tare da mika su asibitoci daban-daban a cikin birnin Kano sakamakon shakar iska mai guba da suka yi
  • Wani bututun kemikal ne 'yan kyadi suka fasa a rukunin masana'antu na Sharada da ke cikin Kano, hakan yasa jama'a suka dinga faduwa magashiyyan
  • An bayyana cewa, hukumomin SEMA, NEMA da na Red Cross ne suka dinga kwashe mutane suna mikawa asibitin Murtala, Ja'en da na Sharada

Kano - Mutum dari biyu da daya mazauna Sharada Kwatas a jihar Kano aka kwantar da su magashiyyan a asibitoci sakamakaon shakar mugunyar iska da suka yi daga wasu karafuna da aka fasa.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa, an gaggauta mika wadanda lamarin ya ritsa da su zuwa asibitin kwarraru na Murtala Muhammad, Asibitin rukunin masana'antu na Sharada da Asibitin Ja'en, domin samun taimakon masana kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Kwana Kadan Zaben Fidda Gwani Na Yan Takarar Shugaban Kasa a APC

Shugaban Hukumar Taimakon Gaggawa ta kasa na yankin Kano, Nuraden Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga NAN a jihar Kano.

Kano: Mutum 201 na Kwance Rai a Hannun Allah a Asibiti Bayan Shakar Kemikal a Sharada
Kano: Mutum 201 na Kwance Rai a Hannun Allah a Asibiti Bayan Shakar Kemikal a Sharada. Hoto daga premiumtimsng.com
Asali: UGC
"Fashewar bututun kemikal din ya faru ne a ranar Juma'a wurin karfe 4 na yamma a rukunin masana'antu na Sharada. Wadanda suka shake shi sun fadi ba su san inda kansu ya ke ba," Yace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau, Sani Muhammad, ya ce wadanda suka fadi warwas sun rasa inda kansu ya ke bayan sun shaki muguwar iska daga bututun da masu sana'ar kyadi suka fasa.

Ya ce kemikal din da ke bututun ya shiga iska kuma ya bugar da duk wadanda suka shaka.

Shugaban asibitin kwararru na Murtala Muhammad, Hussaini Muhammad, ya ce sun karba sama da mutum 70 amma yanzu kusan 65 daga ciki an samo kansu.

"Mutum 35 an kai su asibitin Sharada yayin da 96 aka mika su asibitin Ja'en," yace.

Kara karanta wannan

Kano: Gobara Ta Kashe Mahaifiya Da Ɗanta Mai Shekaru 3 a Gidansu

A daya bangaren, ministan jin kai, tallafi da walwalar 'yan kasa, Sadiya Faruk, ta ziyarci wasu daga cikin wadanda ke kwance a asibitoci.

Babban sakataren ma'aikatar ta, Nasir Sani-Gwarzo ne ya wakilce ta.

Ministar ta jnjinawa hukumomin asibitocin, NEMA, SEMA da Red Cross kan taimakawa jama'a da suka yi.

Ta tabbatar da cewa ma'aikatar za ta taimakawa wadanda lamarin ya ritsa da su.

Wani abu mai fashewa ya sake tashi a wata jihar arewacin Najeriya

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Kogi a ranar Lahadi ta tabbatar da fashewar wani abu a garin Kabba da ke karamar hukumar Kabba-Bunu ta jihar.

Kakakin rundunar, William Ovye-Ayaz, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Lokoja, ya ce babu wanda ya rasa ransa.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya ce fashewar abun ya faru ne a wata mashaya ta Omofemi da ke Kwatas din Okepadi, Kabba, wurin karfe 9:15 na daren Lahadi.

Kara karanta wannan

Uwa da 'yayanta sun kashe maigida mai rowa saboda cin gadonsa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel