ASUU: Gwamnatin Buhari ta yi kwana da kudaden 'yan Najeriya, za su kashe a zabe

ASUU: Gwamnatin Buhari ta yi kwana da kudaden 'yan Najeriya, za su kashe a zabe

  • Kungiyar malaman jami'a ASUU ta zargi gwamnatin Najeriya da tattara kudaden 'yan Najeriya tare da amfani dasu inda bai dace ba
  • ASUU ta bayyana hakan ne ta bakin wani shugabanta da ya zanta da gidan rediyo a Ibadan ta jihar Oyo
  • Ya kuma bayyana cewa, tsarin IPPIS da ake son kakabawa malaman jami'a wani tsari ne da ba zai haifar da da mai ido ba

Ibadan, Oyo - Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ta zargi jiga-jigan siyasar Najeriya da kwashe kudaden Najeriya gabanin babban zaben 2023 maimakon magance matsalolin da ke addabar ilimi a kasar.

Shugaban kungiyar ASUU, reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa gwamnati ta koma tattaunawa da kungiyar duk da cewa sabanin yarjajeniyar farko ne, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

ASUU ta sake bayani kan gwamnati
ASUU: Gwamnatin Buhari ta yi kwana da kudaden 'yan Najeriya, za su kashe a zabe | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewarsa, gwamnati da ASUU za su duba daftarin yarjejeniyar 2009 ta ASUU/FGN wacce tawagar gwamnati ta fara tare da ASUU a 2007 kuma aka kammala shi a watan Mayu, 2021.

Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta ci gaba da koka cewa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da daftarin yarjejeniyar na tsawon watanni 9, saboda haka kungiyar ta nisanta kanta da duk wata tawagar Gwamnatin Tarayya da ta sake kafawa domin bude wata tattaunawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IPPIS tsarin damfara ne, inji ASUU

Akinwole, yayin da bayyana a gidan rediyo a Ibadan, ya bayyana cewa kungiyar ta samu hujjar kin amincewa da tsarin biya na IPPIS wai kawai don ta sabawa tsarin jami’o’i ba, sai dai saboda gano ana son amfani da ita wajen damfarar Najeriya.

Ya yi nuni da cewa, idan har akanta janar na tarayya da aka dakatar zai iya karkatar da naira biliyan 170 duk da manhajar, hakan ya nuna cewa an samu karin hanyoyin zamba a ofishin Akanta Janar na tarayya, inji BusinessDay.

Kara karanta wannan

Neman Kafa Shari'a: CAN Ta Buƙaci Gwamnatin Tarayya Ta Kama Wasu Malaman Addinin Musulunci a Taraba

Akinwole ya bayyana cewa, abin takaicin shi ne, an yi zargin cewa wani mutum daya ne a gwamnati ya karkatar da wasu makudan kudade da ke kusa da adadi na shekara da za a yi amfani da su wajen farfado da jami’o’in gwamnati kusan 100 a duk shekara.

A bangare guda, ya yi kira ga hukumar EFCC da ci gaba da bincike don gano gaskiyar inda aka kai kudin Najeriya tare da tabbatar da dawo dasu.

Dan takarar shugaban kasa ya tono sirri: Ba dan ni ba da Buhari ya sha kaye a zaben 2015

A wani labarin, daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya jagoranci gwagwarmayar siyasar da ta kai ga hayewar shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a 2015.

Tinubu ya kuma ce shi ya kawo Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gumi ya bukaci FG ta kafa ma'aikatar harkokin makiyaya don jin kokensu

Ya yi magana ne a dakin taro namasaukin shugaban kasa da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga deliget din jam’iyyar APC gabanin zaben fidda gwani na jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel