Bidiyon Atiku da iyalansa suna kwasar rawa bayan nasararsa a zaben fidda gwanin PDP

Bidiyon Atiku da iyalansa suna kwasar rawa bayan nasararsa a zaben fidda gwanin PDP

  • Bidiyon Atiku Abubakar, 'dan takarar shugabancin kasa a zaben 2023 a karkashin jam'iyyar PDP ya bayyana yana kwasar rawa cike da nishadi
  • Ba 'dan takarar kadai aka hango a wurin ba, an ga matarsa tare da wasu da ake kyautata tsammanin 'ya'yan sa ne da kuma abokan arziki
  • Atiku ya bayyana sanye da karamar rigar T-Shirt da dogon wando inda ya ke rangaji tare da tafa hannu duk a cikin nishadi da annashuwa

Bidiyon tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma 'dan takarar shugabancin kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana yana kwasar rawa tare da iyalansa.

Atiku da iyalansa sun fada tsananin murna da nishadi sakamakon nasarar da ya samu na yin caraf da tikitin takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Abin da Buhari ya fada wa gwamnonin APC kan zakulo magajinsa

Bidiyon Atiku da iyalansa suna kwasar rawa bayan nasararsa a zaben fidda gwanin PDP
Bidiyon Atiku da iyalansa suna kwasar rawa bayan nasararsa a zaben fidda gwanin PDP. Hoto daga Duoye Diri
Asali: Facebook

A gajeren bidiyon da @HoeGee_Tyla, wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, ya wallafa a shafinsa, an ga Atiku tare da iyalainsa cike da annashuwa sun kwasa rawa.

Bidiyon wanda ya bayyana tare da sautin waka, ya nuna Atiku sanye da farar riga T-Shirt da wando dogo mai launin toka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A tare da dan takarar da ya lallasa fitattun 'yan siyasa a zaben fidda gwanin da aka yi a kwanakin karshen makon da ya gabata, an ga matarsa da wasu da ake kyautata tsammanin 'ya'yansa.

A gabansu akwai farantiai dauke da kayan ciye-ciye da ruwa tare da sauran mutane da ke kaiwa da kawowa tamkar a wurin liyafa.

Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

A wani labari na daban, wata dabara da aka yi tsakanin ranar Juma'a da daren Asabar ne ya dakatar da abun da wata kila za a iya yi wa lakabi da babbar nasara ga gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP na zaben 2023.

Daga karshe dai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ne ya zama zakaran gwajin dafi da kuri'u 371 a cikin 767 na wakilan jam'iyyar da aka tantance a wurin zaben, Premium Times ta ruwaito.

Wike ya samu kuri'u 237 inda yazo na biyu, wanda Bukola Saraki ya biyo bayansa da kuri'u 70, Udom Emmanuel ya samu kuri'u 38, Bala Muhammad kuri'u 20, Pius Anyim guda 14, a karshe Sam Ohuabunwa ya sama kuri'a daya tak.

Asali: Legit.ng

Online view pixel