Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani

Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani

  • Wasu dabaru da aka dauki lokaci ana yi daga ranar Juma'a zuwa daren Asabar ne ya dakatar da abunda za a iya kira da babbar nasara ga gwamnan jihar Ribas a zaben fidda gwanin PDP
  • Sai dai Atiku Abubakar da ya zama zakaran gwajin dafi a zaben, ya yi nasara ne sanadiyyar yadda wasu jiga-jigai suka yi ruwa da tsaki tare da janye masa don ganin ya kawo labari
  • Majiyoyi sun tabbatar da yadda Wike ya yi barin Naira a wajen don ganin ya kawo labari a zaben, duk da mutane da dama sun yi tunanin zai janye

FCT, Abuja - Wata dabara da aka yi tsakanin ranar Juma'a da daren Asabar ne ya dakatar da abun da wata kila za a iya yi wa lakabi da babbar nasara ga gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP na zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Daga karshe dai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ne ya zama zakaran gwajin dafi da kuri'u 371 a cikin 767 na wakilan jam'iyyar da aka tantance a wurin zaben, Premium Times ta ruwaito.

Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani
Yadda Atiku ya yi amfani da dabara daf da mintin karshe, ya doke Wike a zaben fitar da gwani. Hoto daga Duoye Diri
Asali: Facebook

Wike ya samu kuri'u 237 inda yazo na biyu, wanda Bukola Saraki ya biyo bayansa da kuri'u 70, Udom Emmanuel ya samu kuri'u 38, Bala Muhammad kuri'u 20, Pius Anyim guda 14, a karshe Sam Ohuabunwa ya sama kuri'a daya tak.

Sai dai, za a iya alakanta samun nasarar da Atiku ya yi da yadda tsohon shugaban kasa, tsohon shugaban hafsin soji na kasa, tsoffin manyan soji, tsoffin gwamnonin arewa, shugabannin jam'iyyar PDP na arewa da tsohon shugaban binciken sirri da suka yi ruwa da tsaki wajen dakile gwamnan jihar Ribas din, wanda wani rahoton sirrin ya tabbatar da yadda yafi kowa kashe kudi a zaben fidda gwanin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Labari ya bazu kafin fara zaben fidda gwanin a kan yadda Wike zai iya kashe ko nawa ne don ya ga ya yi nasara.

"Su suka yanke shawarar cewa, dole mu dakatar da wannan tahalikin," wata majiyar cikin gida ta bayyana wa Premium Times a daren Asabar.
"Ba su hangi Wike a matsayin wanda ya cancanci zama shugaban kasa ba, sun yi imani da cewa zai karaya ya janye," majiyar ta kara bayyanawa.

Wani bangare na wasu masu zartarwa sun gana da 'yan takarar shugaban kasa na arewa guda biyar don ganin wani ya janye a cikinsu amma Muhammad Hayatu-Deen ne kadai ya amince da kudurinsu, don ya janye ya bar wa Atiku.

Hakan bai sa sun yi kasa a guiwa wajen cigaba da hura wa sauran wuta ba, har sai da gwamnan jihar Sakkwoto, Aminu Tambuwal ya sanar da janyewarsa gami da umartar wakilansa da su zabi Atiku. A kiyasin da su ka yi, raba kuri'un 'yan takarar arewa zai sa gwamnan Ribas ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP

Kamar yadda hadimin gwamnan ya bayyana:

"Mai gida ya ce bai taba shiga cikin wani yanayi na damuwa irin wannan ba a gaba daya rayuwarsa. Sun shaida masa cewa makomar jam'iyyar ya danganta da irin matakin da mai gida ya dauka.
"Haka zalika, sun ce APC na yi wa Wike aiki a bayan fage saboda sun yi imani za a yi saurin nanashi da kasa a zaben," a cewar hadimin gwamnan.

Ko a lokacin da ya shigo wurin zaben, Tambuwal bai riga ya tsaida ra'ayinsa na janyewa ba. Daga baya ya yi hakan kafin wakilan jam'iyyar su fara zaben, inda ya umarci magoya bayansa da su zabi Atiku.

Wasu masu kiyasin siyasa suna ganin janyewar da Tambuwal ya yi ne daga wasan ya taimaka wa tsohon mataimakin shugaban kasar.

Gwamnan jihar Sakkwoto, wanda ya nemi tiketin bayan zaben shekarar 2019 ya yi kamfen matukar, sannan a sakashi a cikin manyan manema tiketin.

Kara karanta wannan

Zaɓen Fidda Gwanin APC: Da Ƙyar Na Sha, Dole Na Tsere Don Kada a Kashe Ni, In Ji Ɗan Majalisa

'Yan jam'iyyar sun ce ya tattara kuri'u musamman daga yankin , arewa maso yamma, wacce ke da wakilan jam'iyyar da suka fi yawa a fadin kasar, da wasu daga cikin jihohin fadin kasar.

Bacin ya janye, da ya raba kuri'un arewa wanda watakila ya budewa Wike hanyar samun damar amsar tiketin.

Kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana, kayen da Wike ya samu ya kawo natsuwa a cikin jam'iyyar, saboda yadda aka siffanta shi da rago wanda ya dogara da amfani da dukiya mai tarin yawa wajen ganin ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP.

Wike ya bar filin zaben fidda gwanin a daren Asabar tun daga lokacin da ya gane karara ya sha kaye a wasan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel