Rayuwata na cikin hadari a Kurkuku, Abba Kyari ya bayyanawa kotu

Rayuwata na cikin hadari a Kurkuku, Abba Kyari ya bayyanawa kotu

  • Abba Kyari ya sake gurfana gaban kotu dake birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 26 ga Mayu, 2022
  • Babban jami'in dan sandan da aka dakatar yace ana yiwa rayuwarsa barazana a kurkuku Kuje, inda aka jefashi
  • Karo na biyu, lauyoyinsa sun gabatar da bukatan a sake shi don ya tafi gida sannan a cigaba da karar, watau a bashi beli

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Dakataccen mataimakin kwamishanan yan sanda, Abba Kyari, ya bukaci kotu ta bashi beli saboda rayuwarsa na fuskantar hadari cikin gidan yari.

Lauyansa, Dr. Onyechi Ikpeazu (SAN), ya gabatarwa babbar kotun tarayya bukatar a ranar Alhamis, rahoton Vanguard.

Ya ce sun bukaci hakan ne saboda rayuwar Abba Kyari na cikin hadari.

Lauyan ya bukaci kotu ta taimaka ta baiwa Kyari beli saboda kada a kashe shi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Amma lauyan gwamnati, Joseph Nbona, ya nuna rashin amincewarsa da hakan in da yace bai samu labarin haka ba kuma ba'a bashi nashi kwafin kudirin ba, a kotu kadai ya ji ana fadi.

A riwayar ChannelsTV, Alkali mai shari'a, Emeka Nwite, ya yanke cewa za'a dage zaman don bangarorin biyu su tattauna tsakaninsu kuma abi tsari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkali daga bisani ya dage zaman zuwa ranar 14 ga Yuni, 2022 don sauraron lamarin belin.

Abba Kyari ya bayyanawa kotu
Rayuwata na cikin hadari a Kurkuku, Abba Kyari ya bayyanawa kotu Hoto: The Nigerian Police Force
Asali: UGC

Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari

Jami'an gidan yari suna tunanin mayar da jami'in 'dan sanda Abba Kyari daga gidan yarin Kuje zuwa hannun jami'an tsarin farin kaya bayan wasu daga cikin abokan zamansa sun yi yunkurin halakasa sakamakon zarginsa da rashin gaskiya wajen bada cin hanci don a samar musu da kwangila a lokacin da yake kan aiki.

Kamar yadda wasu takardun cikin gida da Premium Times ta samu damar gani suka bayyana, an kai masa harin ne a 4 ga watan Mayu, watanni bayan kama Kyari da laifin safarar miyagun kwayoyi. Maharansa sun kai kimanin 190, a cewar wani jami'i, kuma da yawansu an kai su gidan yarin ne saboda harkallar miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel