Yan bindiga sun sako matar da ta shiga daji taimakawa Fulani, sun rike diyarta da direba

Yan bindiga sun sako matar da ta shiga daji taimakawa Fulani, sun rike diyarta da direba

  • Bayan kimanin makonni uku cikin daji, yan bindiga sun saki Lakcarar Kadpoly da suka sace a Kaduna
  • Yan bindigan sun yi garkuwa da ita ne kwanakin bayan yayinda ta shida daji taimakon marasa karfi
  • Ba'a bayyana adadin kudin da aka biya kudin fansa ba

Kaduna - Malama a kwalejin fasahar KadPoly wacce yan bindiga suka sace lokacin da ta shiga daji rabawa Fulani kayan azumi, Dr Rahmatu Abarshi, ta samu kubuta.

A watan Afrilu, yan bindiga sun saceta tare da diyarta da direbanta.

Shugaban kamfanin Liberty TV da safiyar Alhamis ya tabbatar da labarin cewa an sako ta.

A cewarsa:

"An sak Lakcarar amma diyarta, Ameerah da direbanta har yanzu na hannun yan bindigan"

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr Abarshi
Yan bindiga sun sako matar da ta shiga daji taimakawa Fulani, sun rike diyarta da direba Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Adadin mutanen da ake kashe da wadanda akayi garkuwa dasu a Kaduna cikin watanni 3

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana damuwarsa bisa yawaitan yan ta'adan Ansaru da na Boko Haram a jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana cewa hakazalika akwai sabon alaka dake gudana yanzu tsakanin yan bindiga masu garkuwa da mutane da yan Boko Haram.

A cewarsa, wannan alaka ta haifar da harin da aka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga Maris, 2022.

Shi kuma Kwamishanan tsaron, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa akalla mutum 360 aka kashe sakamakon hare-haren yan bindiga kuma an yi garkuwa da mutane 1,389 tsakanin watar Junairu da Maris na shekarar nan.

A cewarsa, mazabar tsakiyar Kaduna wannan kashe-kashe da hare-hare suka fi aukuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel