Ku daina cin Suya, Balango, tsire, suna kawo cutar kansa: Likita

Ku daina cin Suya, Balango, tsire, suna kawo cutar kansa: Likita

  • Aproko Doctor ya sake baiwa yan Najeriya shawara kan abinda yake ganin na da muhimmanci ga kiwon lafiyarsu
  • Masani kiwon lafiyan a ya shawarci jama'a su daina cin naman da aka gasa da hayaki a fili
  • A baya, Aproko Doctor ya baiwa matasa shawara su daina shan magungunan karin girman al'aura

Wani masani ilmin kiwon lafiya, Dr. Chinonso Egemba, ya gargadi yan Najeriya kan cin namar Suya da bai gas sosai ba asaboda hakan kan haifar da citar Daji (Kansa).

Likitan wanda aka fi sani da ‘Aproko Doctor’ a kafafen ra'ayi da sada zumunta ya yi bayanin cewa akwai sinadarin kemikal dake hawa kan nama irin aka gasa kan hayaki.

A jawabin da ya saki a shafinsa na Instagram @aproko_doctor, yace idan aka gasa kan hayaki, sinadaran hydrocarbon.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Yace:

"Idan ka gasa nama a fili, akwai polycyclic aromatic hydrocarbons ko heterocyclic amines. Wadannan sinadarai na haifar da kwayoyin cuta dake lalata DNA, kuma lalacewar DNA na kaiwa ga cutar Daji."
"Idan kuma aka gasa naman sosai har wasu bakaken gawayi suka hau kan namar, mutum zai fi saurin kamuwa da cutar daji."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An gano cutar dajin ciki, mazakura, da mara na da alaka da wadanann sinadarai."
"Ku tabbatar da cewa duk naman da zaku ci ba gasawa aka yi ba, zaku iya soyawa ko gasawa a cikin oven."

A cewar sashen ilmin lafiya ta jami'ar Illinois,

"Ana samun Polycyclic aromatic hydrocarbon ne idan aka kona abu. Sukan haifar da cutar daji kuma suna illata idanu, koda da hanta."
Ku daina cin Suya, Balango, tsire, suna kawo cutar kansa: Likita
Ku daina cin Suya, Balango, tsire, suna kawo cutar kansa: Likita Hoto: @aproko_doctor
Asali: UGC

Namiji na kaiwa shekaru 21 azzakarinsa ya daina girma, Ku daina shan magani: Likita

Kara karanta wannan

'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi

A baya, Aproko Doctor ya bayyana cewa mutum na kaiwa shekaru 21 azzakarinsa ya daina girma.

Likitan, wanda ya shahara da baiwa mutane shawara a Tuwita, ya bayyana hakan ne a bidiyon da ya saki inda yake baiwa matasa shawara su daina sayan magungunan kara girman mazakuta.

A cewarsa, mutum na kaiwa shekaru 21, babu magananin bature ko na gargajiyan da zai kara masa girman al'aurarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel