Namiji na kaiwa shekaru 21 azzakarinsa ya daina girma, Ku daina shan magani: Likita

Namiji na kaiwa shekaru 21 azzakarinsa ya daina girma, Ku daina shan magani: Likita

  • Wani shahrarren Likita ya yi kira ga matasa su daina yunkurin kara tsayin mazakutarsu karfi da yaji
  • Aproko Doctor yace babu hujjar da ta tabbatar da cewa wadannan kwayoyi na kara girman al'uarar
  • A cewarsa, wadannan magunguna na taimakawa wajen lalata kodar matasa

Dr Chinonso Egemba, wanda aka fi sani da Aproko Doctor a manhajar Tuwita ya bayyana cewa mutum na kaiwa shekaru 21 azzakarinsa ya daina girma.

Likitan, wanda ya shahara da baiwa mutane shawara a Tuwita, ya bayyana hakan ne a bidiyon da ya saki inda yake baiwa matasa shawara su daina sayan magungunan kara girman mazakuta.

A cewarsa, mutum na kaiwa shekaru 21, babu magananin bature ko na gargajiyan da zai kara masa girman al'aurarsa.

A cewarsa:

"Idan kana kallon wannan bidiyon kuma shekarunka sun kai 21, azzakarinka ya daina girma."

Kara karanta wannan

Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu

"Ina fadin haka ne saboda masu neman maganin kara girman azzakari."
"Babu wani magani ko itace da ke kara girman mazakuta."
"Wadannan abubuwan da kuke saya na lalata muku 'koda. Shin ka san me maganin ya kunsa? Amma kuna sha."

Likita
Namiji na kaiwa shekaru 21 azzakarinsa ya daina girma, Ku daina shan magani: Likita Hoto: @aproko_doctor
Asali: UGC

Aproko Doctor ya karkare jawabin da cewa gwanda mutum ya cigaba da manejin abinda yake da shi kada ya sayawa kansa wani sabon matsala.

Kalli bidiyonsa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel