'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi

'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi

  • Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna damuwarta akan zargin batancin da ake yi wa wata a Jihar Bauchi jiya inda ta ce sam ba za ta lamunci a dinga halaka mata mutane ba
  • Shugaban kungiyar na reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ya saki wata takarda inda ya ce wajibi ne gwamnati da jami’an tsaro su dauki mataki kafin rigima ta barke
  • A cewar Hayab, an fito da sabon salo ne na amfani da kalmar batanci wurin halaka jama’a inda ya zargi samari musulmai da kulla sharrin batanci ga ‘yan matan da su ka nemi lalata da su suka ki yarda

Kaduna - A jiya ne Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta nuna bacin ranta dangane da zargin wata da batanci da aka yi a Jihar Bauchi, inda ta ja kunne akan cewa ba za ta lamunci kisa da sunan batanci ba, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wata Mata Ta Sake Zagin Annabi a Bauchi, Matasa Sun Bazama Nemanta, Sun Ƙona Gidaje Sun Raunta Fasto

Kungiyar ta CAN kalubalanci gwamnati da kuma jami’an tsaro akan su yi gaggawar daukar matakin da ya dace akan tozarta kundin tsarin mulkin da ake yi kafin gagarumin tashin hankali ya barke wanda za a kasa dakatar da shi.

Zagin Annabi: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba, CAN Ta Ja Kunne
Zagin Annabi: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba, CAN Ta Yi Gargadi. Hoto: Leadership.
Asali: UGC

A wata takarda wacce shugaban kungiyar na reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph John Hayab ya saki, ya ce CAN ta kula da yada ake amfani da sunan batanci a arewacin Najeriya ana halaka wadanda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ba su karasa halakawa ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce an dade ana cutar da kiristoci musamman na arewa

Leadership ta nuna inda Hayab ya ce:

“Ta ina za ka sanya adalci a lamarin da ya faru a Sokoto, da kuma zargin karya da aka yi a Borno na wani Babachir Lawal da wani jarumin fim din arewa wanda mu ke da rahotonsa na batanci da ya yi akan Jesus amma ya yi saurin saukewa daga yanar gizo don ya rufa wa kansa asiri kafin ya fito ya maka zargin karya akan Bababchir Lawal, tsohon SGF, kuma yau mun wayi gari da wani tashin hankalin a Bauchi duk da sunan batanci.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

“Mun san cewa wasu shaidun batancin na karya ne kuma an hada su ne musamman don tayar da tarzoma da cutar da ‘yan mata masu karancin shekaru, masu kamun kai idan wasu mazan dayan addinin sun neme su da lalata sun ki amincewa. Daga nan sai a shirya kage da sunan batanci akansu.
“CAN ta na mamaki idan wa’azin da mu ke gani na kwanan nan dangane da batanci da wasu malaman musulunci su ke yi akan abin da Qur’ani ya tanadar wa wanda ya yi batanci ba bayyananen abu ba ne a cikin musulmai?”

Hayab ya shawarci malamai da jan kunnen jama’a akan daukar doka a hannunsu

Shugaban CAN din ya ci gaba da cewa Kiristocin Najeriya, musamman na arewa sun dade su na fuskantar cutarwa amma duk da haka su ke ci gaba da kawance da kuma nuna soyayya ga musulmai.

A cewarsa, yanzu sabon salon da aka kirkira don samun damar halaka kiristocin kirki shi ne amfani da batanci, kuma CAN ba za ta lamunci hakan ba.

Kara karanta wannan

Ba Ni Da Kuɗi Amma Ina Tausayin Ƴan Najeriya, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC, Fayemi

Ya yi kira ga malaman addinai akan su dinga sanar da mutane illar daukar doka a hannunsu da kuma halaka dan uwanka mutum akan ko wanne laifi ne ya yi maka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel