Abun Tausayi: An tsinci gawar matashiya yar shekara 25 cikin wani yanayi a Jos

Abun Tausayi: An tsinci gawar matashiya yar shekara 25 cikin wani yanayi a Jos

  • Mutane sun gano gawar wata mace matashiya yar kimanin shekara 25 da aka kashe kuma aka yarda gawarta a Rayfield Resort jihar Filato
  • Wani shaida da ya ga gawar matashiyar ya bayyana cewa an cire wasu sassan jikin gawar, da yuwuwar masu asiri suka kasheta
  • Kakakin hukumar yan sanda na jihar Filato ya ce sun samu rahoto amma ba gaskiya bane maganar an cire wasu bangarorin gawar

Jos, jihar Plateau - An gano gawar wata matashiyar budurwa da aka watsar a Rayfield Resort ba bu wasu sassan jikinta a yankin ƙaramar hukumar Jos ta kudu dake cikin jihar Filato.

Daily Trust ta rahoto cewa Mamaciyar, wacce daga baya aka gano sunanta, Francisca Choji, tana zaune tare da iyalanta a yankin Gada Biyu a ƙaramar hukumar Jos ta arewa.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Taswirar jihar Filato.
Abun Tausayi: An tsinci gawar matashiya yar shekara 25 cikin wani yanayi a Jos Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa matashiyar ta bar gida ne zuwa wani wuri da ba'a bayyana ba amma daga bisani sai gawarta aka tsinta ranar Lahaɗi da safe.

Wani shaida da ya ga abun da ya faru ya ce alamu sun nuna an kashe ta ne bisa dalilin tsafi kasancewar babu wasu sassan jikinta a gawar da aka tsinta.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Amma a ɓangaren su, kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya ce sun samu labarin ganin gawa a Rayfield Resort.

Sai dai kakakin yan sandan ya musanta cewa an cire wasu sassa a jikin gawar, inda ya ce:

"Mun sami rahoton ganin wata gawa a Rayfield Resort amma ba bu wasu sassa da aka cire a jikin gawar. Hukumar yan sanda ta duƙufa bincike kan musabbabin da ya jawo mutuwar matashiyar."

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

Bincike ya nuna cewa tsakanin watan Disamba, 2021 zuwa watan Janairu, 2022, gawar matasan yan mata biyu aka gano ba rai a wurare daban-daban tare da cire wasu sassan jikin su a Jos.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya ce ba ya iya bacci da daddare saboda matsalar tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ko kaɗan ba ya iya kwantawa ya yi bacci saboda matsalar tsaron da ta dami Najeriya.

Jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a Barikin Mambila, Buhari ya ce ba zai raga wa yan ta'adda ba har sai ya ga bayan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel