2023: Jerin Hadimai, Mataimaka, da Mukarraban Gwamnati Buhari 7 da za su tsaya takara

2023: Jerin Hadimai, Mataimaka, da Mukarraban Gwamnati Buhari 7 da za su tsaya takara

  • Akwai wasu manyan masu rike da mukamai a gwamnatin tarayya da za su ke shirin yin takara
  • Daga cikin wadanda za su nemi kujerun siyasa shi ne Mai girma mataimakin shugaban Najeriya
  • Akwai Ministocin tarayya da za su nemi takarar shugaban kasa, wasu za su yi takara a jihohinsu

Mun tattaro jerin daga wani rahoto da ya fito daga jaridar The Cable. Bayan nan mun kara da sunayen wasu hadimai da ake aiki a fadar shugaban Najeriya.

1. Yemi Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo zai nemi takarar shugaban kasa a zaben 2023. Mataimakin shugaban kasan yana gani shi ya fi dacewa da ya karbi ragamar mulkin Najeriya.

2. Rotimi Amaechi

Rotimi C. Amaechi yana cikin Ministocin da za su nemi tutar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC. Tun 2015 yake rike da kujerar babban Ministan sufuri.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yau masu harin kujerar Shugaban kasa a PDP za su san matsayin takararsu

3. Chukwuemeka Nwajiuba

The Cable ta ce Chukwuemeka Nwajiuba shi ne Minista na uku da yake sha’awar zama shugaban Najeriya. A halin yanzu Nwajiuba shi ne karamin Ministan harkar ilmi.

Gwamnati Buhari
Shugaba kasa wajen taron FEC Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

4. Chris Ngige

Babban Ministan kwadago na kasa, Sanata Chris Ngige zai nemi shugabanci a zabe mai zuwa. Tsohon gwamnan na Anambra yana cikin jiga-jigan ‘yan APC.

Takarar Gwamna

5. Abubakar Malami

Wani Minista da yake sha’awar zama gwamna a zaben 2023 shi ne Abubakar Malami. Alamu na nuna Ministan shari’ar zai nemi tikitin zama gwamnan jihar Kebbi.

Hadimai da sauran masu mukamai

6. Bashir Ahmaad

A baya an ji cewa Bashir Ahmaad ya shiga siyasa gadan-gadan, yana so ya wakilci mutanen Gaya/Albasu/Ajingi da ke jihar Kano majalisar wakilan tarayya

7. Ita Enang

Kara karanta wannan

Rochas Okorocha da wasu Sanatoci 3 da za su yi takarar Shugaban kasa a zaben 2023

Ana da labari Mai ba shuagaban Najeriya shawara a kan harkokin Neja-Delta, Sanata Ita Enang zai nemi kujerar Gwamnan a Akwa Ibom a karkashin jam’iyyar APC.

‘Yan jita-jita

Akwai wadanda ake rade-radin za su yi takara ko da nan gaba. A wannan sahu akwai Isa Pantami, Tunde Fashola, Ogbonoyya Onu, Mohammed Muhammad.

Akwai irinsu Ministan wasanni da matasa Sunday Dare, Ministan ma’adanai, Uche Ogah. Sai tsofaffin gwamnonin da ke FEC, Godswill Akpabio da Timipre Sylva.

Ana jita-jitar gwamnan CBN, Godwin Emfiele ya na neman mulki, sai dai ya karyata wannan labari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel