Watan Ramadan: 'Yan Sandan Kano Sun Hana Yin 'Tashe' a Jihar, Sun Bada Dalili

Watan Ramadan: 'Yan Sandan Kano Sun Hana Yin 'Tashe' a Jihar, Sun Bada Dalili

  • Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta hana yin wasan Tashe wanda aka saba yi duk shekara a kwanakin 10 na tsakiyan watan Ramadan
  • Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana hakan ta wata takarda wacce ya saki inda ya ce kwamishinan ‘yan sanda ne ya hana
  • A cewarsa, akwai bata-garin da suke amfani da damar Tashe wurin yin miyagun ayyuka kamar kwace da shaye-shaye hakan yasa suka yi wa tufkar hanci

Kano - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta hana yin wasan ‘Tashe’, al’adar da aka saba yi duk shekara da watan Ramadan bayan kwanaki 10 na farkon watan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana hakan a wata takarda wacce ya saki a ranar Litinin 11 ga watan Afirilu, inda ya ce akwai bata-garin da suke amfani da tashe suna tafka barna.

Kara karanta wannan

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

Watan Ramadan: 'Yan Sandan Kano Sun Hana Yin 'Tashe' a Jihar
Watan Ramadan: 'Yan Sandan a Kano Sun Haramta Yin 'Tashe' a Jihar. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai dalilai na matakin

Kamar yadda Kiyawa ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano tana farin cikin sanar da jama’a cewa ta dakatar wasan gargajiya (Tashe) wanda ake yi bayan ranakun farko 10 na watan Ramadan.
“Hakan ya biyo bayan ganin yadda wasu bata-gari suke amfani da damar wurin aiwatar da miyagun ayyuka kamar sara-suka, kwacen wayoyi da shaye-shaye.”

Ita ma Daily Trust ta rahoto cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ma ya yi kira ga mazauna jihar, muasamman iyaye da su ja kunnen yaransu daga keta dokoki.

Rundunar ta bayar da lambobin da za a tuntube ta idan wani abu ya taso

Takardar ta ci gaba da cewa:

“Duk wanda aka kama yana keta dokoki za a ladabtar da shi. Muna yi wa kowa fatan yin azumi lafiya.

Kara karanta wannan

Kano: Rundunar 'yan sanda ta hana tashe a watan Ramadan ta bana a jihar

“Idan akwai wani abu da ya taso na gaggawa, ana iya tuntubar rundunar ta wadannan lambobin, 08032419754, 08123821575, 08076091271. 09029292926 ko kuma a bi wannan adireshin na yanar gizo, “NPF Rescue Me” wanda za a iya samu a manhajar Play Store. Mun gode kuma Ubangiji ya yi albarka.”

Bidiyon Wasu Mutane Biyu Da Suka Bawa Hammata Iska a Masallacin Ka'aba

A wani labarin, Jami'an tsaro na musamman masu kula da aikin Hajji da Umarah a kasar Saudiyya sun fara bincike a kan wasu mutane biyu da suka yi dambe a cikin Massallacin Harami na Makkah, BBC Hausa ta rahoto.

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wasu mutane biyu suna bawa hammata iska a cikin masallacin Makkah, a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel