Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

  • Wani bidiyo ya karada shafuka da zaurukan sada zumunta da sunan an yi ram da ‘yan bindiga a Kaduna
  • Binciken da jami’an tsaro suka gudanar ya tabbatar da cewa wasu makiyaya ne kurum aka kama
  • Rashin fahimta ya jawo rigima ta barke tsakanin Fulani da wasu mutane, har aka rasa rayuwa a Chikun

Kaduna - Sojoji da ‘yan sanda sun yi bayani game da bidiyon da yake yawo a kafafen sada zumunta, da sunan cewa an kama ‘yan bindiga a jihar Kaduna.

A wani rahoto da ya fito a jaridar Leadership ta ranar Litinin, 10 ga watan Afrilu 2022, an ji cewa ba ‘yan ta’adda aka kama kamar yadda mutane su ke tunani ba.

Jami’an tsaro sun yi wannan karin haske yayin da aka yi wani zaman sulhu tsakanin jagororin Gbagyi da kuma al’ummar Fulani da ke Kakura a garin Chikun.

Kara karanta wannan

Ganin saukar bakon jirgin sama: Jami'an tsaro sun bincike dajin Ogbomoso ciki da waje

A cewar jami’an tsaron, binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mutanen da aka gani a bidiyo, makiyaya ne aka yi ram da su, ana tunanin ‘yan bindiga ne.

‘Yan banga ne suka yi kuskuren damke wadannan mutane, bisa zargin cewa su ne ‘yan bindigan da suka kai wa mutanen Kakura farmaki babu gaira-babu dalili.

An yi taro a ofishin Kwamishina

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shugaban karamar hukumar Chikun, Salasi Musa sun samu halartar wannan zama.

Gwamnan Kaduna
Gwamnan Kaduna a wani taro Hoto: @govkaduna
Asali: Facebook

Sauran wadanda aka yi taron da su, sun hada da ‘dan majalisar yankin Chikun, Hon. Ayuba Chawaza, Hakimin Kujama, Stephen Ibrahim da jami’an tsaro.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna, Yekini Ayoku ya shaidawa mahalartan cewa an taba mutanen Gbagyi da na Fulani a harin da aka kai a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga za su ‘kashe’ fasinjojin jirgin kasa, idan Gwamnati ta gaza biya masu bukata

An kashe 'danuwan Mai gari

CP Ayoku ya ce asalin abin da ya faru a makon da ya gabata shi ne ‘yan bindiga sun shiga Kakura, sun hallaka wani ‘danuwan mai garin wannan kauye, Isiaku Karfe.

Miyagun sun kuma kai hari a wani kauyen Fulani, suka dauke dabbobi. Daga nan mutane su ka shiga farautar ‘yan bindigan, su kuma Fulani na neman dabbobinsu.

A sanadiyyar haka sai aka yi kicibis, aka kashe Fulani uku, wasu suka samu rauni daga rikicin. Rahoton ya ce bayan an yi bincike, an fahimci ba miyagu aka kama ba.

Tsageru su na jawo asara

A makon jiya ne Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari ya bayyana a gaban majalisar wakilan tarayya a dalilin fasa layin mai da ake yi a kudancin Najeriya.

Mele Kolo Kyari ya yi tir da aikin masu fasa bututun danyen mai da masu matatan da ba su da rajista, ya ce wannan matsala ta jawo Najeriya ta yi asarar $1.5bn a 2022.

Kara karanta wannan

Nasara: Yadda DSS suka kama wasu mutanen da suka shahara wajen sace kananan yara

Asali: Legit.ng

Online view pixel