A cikin kwanakin nan, N10,000 ba ta isa a yi jar miya, Matashiyar budurwa ta janyo cece-kuce

A cikin kwanakin nan, N10,000 ba ta isa a yi jar miya, Matashiyar budurwa ta janyo cece-kuce

  • Wata mata ƴar Najeriya ta tada ƙura a kafar sada zumuntar Twitter bayan ta ce N10,000 baza ta isa ayi jar miya ba
  • Mutanen da suka caccake ta sun ce babu yadda za a yi mutum ya buƙaci albasar N500 don ya dafa miyar da za ta kare cikin lokaci ƙalilan
  • Akwai waɗanda suka ce ta yi guntun lissafi mai cin kuɗi, saboda wataƙila ta koyi girkin ne a YouTube

Wata matashiyar budurwa mai amfani da @Ore_akiinde a Twitter a ranar Talata, 5 ga watan Maris ta tada ƙura a kafar sada zumunci bayan ta ce a yanzu 10,000 ba za ta isa mutum yin jar miya ba.

Yayin martani ga sukar da mutane suka ma ta, budurwar ta ce tana nufin tun farko kudin siyan kaza, gas din girki, lita daya na mai, da sauran abubuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malaysia za ta daure ko cin tarar 'yan kasa da ke cin abinci da rana a Ramadan

A cikin kwanakin nan, N10,000 ba ta iya isa a yi miya, Matashiyar budurwa ta janyo cece-kuce
A cikin kwanakin nan, N10,000 ba ta iya isa a yi miya, Matashiyar budurwa ta janyo cece-kuce. Hoto daga @Ore_Akinde
Asali: Twitter

Ta bayyana farashin kaza a N4,000. Akwai mutanen da suka yarda da ra'ayinta na cewa N10,000 ba za ta isa mutum ba, duba da yadda farashin komai ya tashi a kasuwa.

Daga lokacin da aka rubuta wannan labarin, wallafar ta janyo sama da tsokaci 2,000, tare da dubbannin jinjina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane sun ƙaryata ta

Legit.ng ta tattaro muku wasu daga cikin tsokacin mutane karkashin wallafar, ga wasu daga cikin tsokacin:

@oluwakore_de criticised her: "Ya kamata ki siya tukunya da ice ki haɗa."
@Attractalfee ya ce: "Cabdijam! wasu daga cikin ku da ke cewa N2,000 kudin tumatur, kodai ba kwa zuwa kasuwa, ko kuma ba kwa girki ko kuma duka biyun!"
@PapaKing73 ya ce: "Wannan shi ne abunda ke faruwa idan ka koyi girki a YouTube."
@abbietayo ya ce: "Mutane ba su san albasar N500 na da tsada a wasu wuraren ba."

Kara karanta wannan

Matar Aure mai juna biyu ta daɓa wa mijinta wuƙa har lahira yana tsaka da bacci kan zai ƙara Aure

@Cowboydada ya ce: "Tun da farko ma dai, bakiyi hayar dakin girkin ba? 10,000 tayi kaɗan."

@d1dowski ya ce: "Gaba ɗaya anguwan za ki dafawa abinci ko me??"
@theAyees ta ce: " Wata sabuwa. Wahala ga matayen da mazajen irin wannan."
@ikeoliwaaaaa ya ce: "Meye ta faɗa ba daidai ba kuma?? gaskiya ƴan Najeriya na da matsala fa. Nawa kayan yaji yake? Mai? Nama ko kifi? kuna da hankali kuwa???"

Bidiyon budurwar da ta dauka nauyin aurenta da saurayinta, sun rabu cikin kwanaki 120

A wani labari na daban, wata bazawara ta bayar da labarin yadda ta yi nadamar aure da darussan da ta koya bayan ta rabu da tsohon mijinta kuma masoyinta.

Matar mai suna June Katei Reeves 'yar asalin kasar Kenya ce wacce ta yi soyayya da tsohon mijinta na tsawo shekaru tara amma aurensu watanni hudu kacal ya yi sakamakon rashin zaman lafiyan da suke fuskanta.

Kara karanta wannan

Sifetan dan sanda ya sheka lahira yana tsaka da 'kece raini' da bazawara a otal

Asali: Legit.ng

Online view pixel