Bidiyon budurwar da ta dauka nauyin aurenta da saurayinta, sun rabu cikin kwanaki 120

Bidiyon budurwar da ta dauka nauyin aurenta da saurayinta, sun rabu cikin kwanaki 120

  • Wata mata 'yar asalin kasar Kenya mai sune June katei Reevs ta bayyana nadamarta kan yadda ta auri tsohon mijinta
  • Mahifiyar da dayan wacce aurensu yayi wata hudu kacal ta ce tana ganin kamar ta watangarar da shekaru 9 na rayuwarta a banza ne
  • Kamar yadda matar mai aiki ta ce, ta siyo zoben aurensu kuma ta dauka nauyin bikin amma hakan bai sa sun samu zaman lafiya ba

Kenya - Wata bazawara ta bayar da labarin yadda ta yi nadamar aure da darussan da ta koya bayan ta rabu da tsohon mijinta kuma masoyinta.

Matar mai suna June Katei Reeves 'yar asalin kasar Kenya ce wacce ta yi soyayya da tsohon mijinta na tsawo shekaru tara amma aurensu watanni hudu kacal ya yi sakamakon rashin zaman lafiyan da suke fuskanta.

Kara karanta wannan

Allah ya tsarkake mani zuciyata, zan iya mutuwa a gobe, matar tsohon shugaban kasa

Bidiyon budurwar da ta dauka nauyin aurenta da saurayinta, sun rabu cikin kwanaki 120
Bidiyon budurwar da ta dauka nauyin aurenta da saurayinta, sun rabu cikin kwanaki 120. Hoto daga Lyn Ngugi
Asali: UGC

June ce tamkar mijin

A wata doguwar tattaunawa da aka yi da Lynn Ngugi, matar 'yar asalin kasar Kenya ta ce duk da ta yi aure, ita ce ta dauka nauyin dawainiya da gidan da kuma mijinta mai jini a jika. Mijinta ba ya kawo komai gidan.

Budurwa da ta kammala digirinta a jami'ar Kenyatta, ta ce hakan ce dama ta kasance tun suna soyayya.

June ta ce ita ke rufawa mijinta asiri ta yadda ta ke kula da gidan amma tana nuna cewa shi ke kula da gidan. Ko a lokacin da ta dauka dawainiyar aurensu, ta nunawa duniya shi ne yayi komai.

Yadda June ta hadu da tsohon mijinta

Matar mai aiki wacce ta zama bazawara mai diya daya, ta ce ta hadu da tsohon mijinta a makaranta a shekarar 2009 kuma sun fara zama tare kuma suka yi soyayya ta tsawon shekaru tara.

Kara karanta wannan

Ta tabbata: Budurwar da ta yi wa Jaruma mai Kayan Mata kwacen miji, ta bayyana

Ta bayyana cewa bazawara ce ta raini tsohon mijinta. June ta ce a wani lokaci da suke soyayya kuma suna samun kalubale, ta yanke hukuncin su haihu domin samun karin dankon soyayya.

Duk da haihuwa da suka yi, lamarin ba ta sauya zani ba har sai da suka rabu a shekarar 2018.

June ta ce sun sake komawa a 2020 kuma sun yanke shawarar yin aure a ranar 19 ga watan Disamban 2020. Sai dai mummunan zama da rashin jituwa ta cigaba bayan sun yi auren da suka kammala amarcin su.

"Auren ya koma wata masifa inda ake fada tare da duka wanda diyarmu ke kallo kuma har aka taba ji mata rauni. Mahaifiyata ta gani saboda ta fara zama tare da mu bayan auren," tace.

Kalla bidiyon labarin June a kasa:

Maza gudunmu suke, ba su neman aurenmu, Mata nakasassu sun koka da rashin mazan aure

A wani labari na daban, shugabar ƙungiyar haɗakar nakasassu ta ƙasa (JONAPWD) na jihar Edo, Ms Ann Ujugo, ta koka game da yadda a Najeriya nakasassun mata ke fuskantar wariya, idan aka zo batun aure.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Bidiyon yadda mata ta shekara tana tara kudi a asusu, ta ga N90 yagaggu

Ta ce, mazan Najeriya basa aurensu, suna barinsu a gwauraye tsawon rayuwarsu, Leadership ta ruwaito.

Ojugo ta fadi hakan ne jiya a Benin City, jihar Edo, yayin zantawa da manema labarai don tunawa da ranar mata ta duniya a ranar 8 ga watan Maris na kowacce shekara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel