Goodluck Jonathan: Yadda ‘Yan Sandan da ke kula da ni, suka mutu nan-take a hadarin mota

Goodluck Jonathan: Yadda ‘Yan Sandan da ke kula da ni, suka mutu nan-take a hadarin mota

  • Wani mugun hadari ya rutsa da tawagar Goodluck Ebele Jonathan a babban birnin tarayya Abuja
  • Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya na hanyar komawa gidansa a Abuja daga filin jirgi ne abin ya faru
  • A jawabin da ya fitar, tsohon shugaban kasar ya ce hadarin ya yi sanadiyyar rasa wasu ‘yan sanda

Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya yi magana bayan hadari ya rutsa da tawagarsa a yammacin Laraba, 6 ga watan Afrilu 2022.

Jaridar Daily Trust a rahoton da ta fitar ta ce hadarin ya auku ne yayin da Goodluck Jonathan yake kokarin komawa gidansa daga filin tashin jirgin sama.

Da yake bayanin abin da ya faru, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ‘yan sanda biyu da ke kula da shi sun mutu nan-take bayan aukuwar hadarin.

Kara karanta wannan

Ya auna arziki: Mummunan hadari ya rutsa da tsohon shugaban kasa Jonathan

Mai magana da yawun bakin tsohon shugaban kasar, Ikechukwu Eze ne ya fitar da jawabi na musamman a madadinsa daga birnin tarayya na Abuja.

Ikechukwu Eze ya ce bayan ‘yan sandan da suka mutu, wasu jami’ai biyu kuma sun samu rauni.

Hadarin ya shafi motar jami’an tsaron da ke da nauyin kula da lafiyar tsohon shugaban kasar ne. Yanzu haka wasu daga 'yan tawagar su na jinya a asibiti.

Goodluck Jonathan
Tawagar motocin shugaban kasa Hoto; www.legit.ng
Asali: UGC

Jonathan bai ji dadi ba

Rahoton ya ce Jonathan ya ji takaicin abin da ya wakana, ya ce wadannan jami’an tsaro da aka rasa, jajirtattu ne wadanda su ka dage a wajen bakin aikinsu.

“Jonathan ya tabbatar da cewa wadanda suka rasu, Sufeta Ibrahim Abazi da Yakubu Toma, kwararrun jami’ai ne da suka jajirce wajen yi wa kasarsu hudima,”

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

“An yi wuf an kai wasu jami’ai biyu da suka samu rauni daga hadarin da ya aukawa motar da ke daukar jami’an tsaron. An kai su asibiti a Abuja, ana kula da su.”
“Ofishin tsohon shugaban kasa ya na aika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da rundunar ‘yan sanda.”
“Dr. Jonathan ya roki Ubangiji ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, tare da yi wa iyalansu da kasa albarka, da kuma ba su hakurin jure wannan rashin.”

- Ikechukwu Eze

Jonathan ya tsira

A jiya aka ji fara jin labari cewa an samu aukuwar hatsarin mota da ya rutsa da ayarin motocin tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan a Abuja.

Kamar yadda aka ji, tsohon shugaban kasar yana cikin koshin lafiya, amma rahotanni sun nuna cewa wasu mukarrabansa sun mutu, wasu sun samu rauni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel