Dausayin Ramadana: Abubuwan da suka faru a tarihi da garabasar dake cikin watan azumi, Sheikh Aminu Daurawa

Dausayin Ramadana: Abubuwan da suka faru a tarihi da garabasar dake cikin watan azumi, Sheikh Aminu Daurawa

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa babban Malamin addinin Musulunci ne mazaunin jihar Kano wanda ya fi shahara wajen bayani kan mas'alolin rayuwa da zamantakewa.

A wannan karo, Malam ya yi bayani kan falalar watan Ramadana

ABUBUWAN DA SUKA FARU A TARIHI DA GARAƁASAR DAKE CIKINSA

1. Allah maɗaukakin sarki ya saukar da Al-Ƙur'ani Mai Girma a cikinsa. Kamar yadda ya zo a cikin suratul bakara; inda Yake cewa:

“Watan Ramadhan ne wanda aka saukar da Al-Ƙur'ani a cikinsa shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu na shiriya da kuma rarrabewa.” (Tsakanin daidai da ba daidai ba).

Lallai haƙiƙa Allah ﷻ Ya zaɓi wannan wata daga cikin watanni ya fifita shi a tsakanin su, Ya zabe shi Ya saukar da Al-ƙƙur'ani a cikinsa.

Kara karanta wannan

Ramadaniyyat 1443: Masu Tauye Mudu (1) tare da Sheikh Dr Sani Rijiyar Lemo

2. A cikinsa ne aka saukar da sauran littattafan da Allah ﷻ Ya saukar ga sauran Annabawa , kamar yadda aka ruwaito a hadisin Wasilata Bn Aska'i, Manzon Allah ﷺ ya ce,

“An saukar da suhufi Ibrahim a dare na farkon watan Ramadhan, an saukar da Attaurah a dare na shida (6) ga watan Ramadhan, an saukar da Injila a sha uku (13) ga watan Ramadhan, an saukar da Al-Ƙur'ani a ashirin da huɗu (24) ga watan Ramadhan.” (3)

3. A cikin watan Ramadhan ne ake buɗe ƙofofin Aljannah.

4. A cikin watan Ramadhan ake rufe ƙofofin wuta.

5. A cikin watan Ramadhan ne ake ɗaure kangararrun sheɗanu macuta.

6. A cikin watan Ramadhan ne ake buɗe ƙofofin rahama.

7. A cikin watan Ramadhan ne ake buɗe ƙofofin sama.

Kara karanta wannan

Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

8. A cikin watan Ramadhan ne mai kira yake kira yana cewa, “Ya kai mai nufin alkhairi ka gabato, ya kai mai nufin sharri ka ja da baya.” (4)

Sheikh Aminu Daurawa
Dausayin Ramadana: Abubuwan da suka faru a tarihi da garabasar dake cikin watan azumi, Sheikh AminuDaurawa Hoto: Mal. Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

9. A kowanne dare akwai waɗanda Allah ﷻ Yake ‘yantawa ya tseratar da su ga barin shiga wuta.

10. Ana amsa addu'a a cikin watan Ramadhan, kuma Allah ﷻ Ya ambata a cikin suratul Baƙarah inda Yake cewa:

“Idan bayi na sun tambaye Ka game da ni ka ce ina kusa, kuma ina amsa kiran mai kira idan ya kirawoni, don haka su amsa min su yi imani da ni, domin su sami shiriya.”

11. An ruwaito hadisi daga Abu Sa'id Al-Khudri da Abu Huraira امهنع الله ضر cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce,

“A kowanne dare Allah ﷻ yana ‘yanta bayi daga shiga wuta, kuma kowanne bawa yana da addu'a da ake amsa masa.”

Kara karanta wannan

Yunƙurin Kisa: Ƴan Bindiga Sun Buɗe Wa Babban Ɗan Majalisar APC Wuta

12. Watan Ramadhan wata ne na zikiri, istigfari, salatin Annabi ﷺ, karatun AlƘur'ani da godiya ga Allah ﷻ. Domin Allah ﷻ yana tsaka da yin bayani a game da azumi sai Ya ce “Domin ku girmama Allah ﷻ saboda Ya shirye ku ko kwa gode masa.” Suratul bakara aya ta 185.

13. Watan Ramadhan wata ne na hakuri da juriya saboda hadisin nan na balaraben ƙauye wanda Abdullahi Ɗan Abbas هنع الله ضر da yake cewa: Manzon Allah ﷺ ya ce,

“Watan azumin Ramadhan watan haƙuri ne, wanda shi ake cewa (shahrus sabri), wato watan haƙuri, da kuma yin azumin kwana uku a kowane wata yana tafiyar da nunkufurcin zuciya wato suna cire tsatsar zuciya, su tsarkake ta ga barin munafirci da kafirci, don haka babu makawa shi watan azumi wata ne na hakuri, juriya, yarda da ƙaddarar da Allah ﷻ ya ɗorama, yin hakuri a kan biyayya gareshi da hakuri jin raɗaɗin yinwa da ƙishi da kuma ƙauracewa hane-hanen Allah ﷻ da bin umarninsa.

Kara karanta wannan

Tunatarwa: Abubuwan da ya kamata kusani masu muhimmanci game da watan Azumin Ramadan

Kuma Allah ﷻ Ya ce: )Ma’ana: “lallai haƙiƙa ana cikawa masu hakuri ladansu ba tare da lissafi ko bincike ba.

14. Azumin watan Ramadhan yana kankare zunubai saboda hadisin Abi Huraira inda yake cewa, Manzon Allah ﷺ yana cewa;

“Juma'a zuwa Juma'a, azumi zuwa wani azumin, waɗannan suna kankare zunubban da suke tsakaninsu idan an nisanci manya-manyan zunubai.”

Watan Ramadhan ana gafarta zunubbai a cikinsa saboda hadisin Abi Huraira wanda yake cewa, Manzon Allah ﷺ ya ce,

“Wanda ya azumci watan Ramadhan yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa abin da ya gabata na zunuban sa. Bukhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel