Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau

Abuja- Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci zaman Tafisirin Al-Qura'ni mai girma a Masallacin fadar shugaban kasa Aso Villa a yau ranar Litinin, 4 ga Afriku, 2022.

Tafsirin Al-Qur'ani wani koyarwan addinin Musulunci ne da aka saba yi kowani watar Ramadana.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed, ya bayyana a shafinsa na Tuwita.

Babban Limamin Masallacin fadar shugaban kasa, Sheikh Abdulwahab Sulaiman, wanda yake tafsirin ya yi Alla-wadai da yan ta'addan da suke amfani da addini wajen kisan kai da diba dukiyan mutane.

Ya yi addu'an Allah ya kawar da wadannan yan ta'adda, yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma annobar Korona, riwayar Vanguard.

Daga cikin wadanda ke hallare Masallacin tare da shugaban kasa akwai amininsa, Mamman Daura; mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu; da sauran wasu makusanta.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An nada Sheikh Nuru Khalid limanci a sabon Masallaci a Abuja

Kalli hotunan:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari
Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau
Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau
Asali: Twitter

Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau
Hotuna: Shugaba Buhari ya halarci zaman Tafsirin AlQur'ani yau
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel